Dirama ta kaure yayinda wanda ake zargi da kisan dalibar UniJos ya kurmance a kotu
- An gurfanar da mutumin da ake zargi da kisan budurwarsa, yar jami'ar tarayya dake Jos, jihar Plateau
- Yayinda ya bayyana a kotu, lauyansa ya bayyana cewa zargin da ake masa ya yiwa kwakwalwarsa nauyi
- Yanzu dai an dakatad da zaman kotun zuwa wani lokaci
Jos - Moses Oko, mutumin da ake zargi da kisan budurwarsa, Jennifer Anthony, dalibar aji uku a jami'ar UniJos ya kurmance cikin kotu yayinda aka gurfanar da shi ranar Litinin.
Alhali lokacin da ya isa kotun tare da iyayensa, suna magana a waje kafin a zo kansu.
Amma diramar ta fara ne lokacin da aka bukaci ya shiga akwatin mai zargi yayi ranstuwa, rahoton DailyTrust.
Da farko Moses Oko ya ki shiga cikin akwatin da kansa, ya wayance kamar bai san abinda ke faruwa ba. Sai da jami'in gandiroba ya shigar da shi, rahoton ya kara.
Yayinda ya shiga cikin akwatin kuma magatakardan kotu ya kira sunansa don yayi rantsuwa, ya ki amsawa, ko kalma guda bai furta ba.
Sai lauyansa Barista Alex Muleng, ya bayyanawa Alkali cewa Moses ya samu matsalar kwakwalwa ne.
A cewarsa:
"Da alamun tuhume-tuhumen da aka yi masa yayi masa nauyi da yawa saboda haka ya samu tabin kwakwalwa."
Kotu ta sake mai garkuwa da mutane kan hujjan yana da tabin hankali lokacin da ya aikata laifin
Wani mutumi da aka kama da laifin sace dan shekara shida ya samu yanci bayan kotu ta gano cewa yana da tabin hankali lokacin da ya aika laifin.
Mai magana da yawun ma'aikatar shari'ar jihar Jigawa, Zainab Baba-Santali, ta bayyana hakan a jawabin da ta saki.
An damke mai garkuwa da mutanen mai suna Safiyanu Rabiu da laifin rabawa yaran makwabta alewa sannan ya sace daya cikinsu.
Asali: Legit.ng