Bayan ƙodarta ta yi ɓatan dabo daga zuwa Saudiyya, za a biya ta N31.8M diyya

Bayan ƙodarta ta yi ɓatan dabo daga zuwa Saudiyya, za a biya ta N31.8M diyya

  • Judith Nankitu, wata mata 'yar asalin kasar Uganda ta dawo daga Saudi Arabia babu koda kuma an tilasta wanda ya dauke ta aiki, Saad Dhafer da ya biya ta diyya
  • Lauyan da ya wakilci kamfanin da ya kai ta Saudi, ya ce sun maka Dhafer a kotu bayan ya yi ikirarin cewa ta tafka hatsarin mota ne
  • Wata kotu ta umarcesa da ya biya ta KSh 8.7 million (N31,825,778.15) kafin daga bisani a gano cewa wata muna-muna aka yi wurin cire kodar

Judith Nakintu, wata mata 'yar kasar Uganda wacce aka cire mata koda a kasar Saudi Arabia ba tare da izninta ba, za a biya ta miliyoyi.

Za a biya wata mata N31.8m diyya bayan an sace mata ƙoda a Saudi Arabia
Za a biya wata mata N31.8m diyya bayan an sace mata ƙoda a Saudi Arabia. Hoto daga Vision Group
Asali: UGC

Labarin hatsari da Judith ta yi

Kamfanin kwadago na Nile Treasure da ya dauka Judith zuwa Jeddah ya ce sun yarda cewa tsohon ubangidanta, Saad Dhafer ya ce wani mugun hatsari ya ritsa da ita.

Kara karanta wannan

Sharri aka min, ina da ciwon sukari da hawan jini: Abba Kyari ya kai karar gwamnati kotu

Bayan samun labarin hatsarin, lauyan kamfanin ya ce sun fara shigar da karar yadda za ta samu a biya ta diyya.

"An shigar da kara a madadinta kuma kotun ta yi hukunci a kan hakan. A hukuncin ranar talatin ga watan Janairu, kotu ta umarci Dhafer da ya biya ta KSh 8.7 miliyan (31,825,778.15) baya ga kudin shigar da kara," lauyan yace.

Daga bisani lauyan ya fitar da wasu takardu da suka hada da rahoton hukumar kula da hadurra inda ya bayyana cewa wani hatsari da ya kashe 'ya'yan ubangidanta biyu ya ritsa da ita.

'Yan fashi sun kacame da rikici suna tsaka da fashi, sun halaka junansu da makamansu

A wani labari na daban, reshe ya juye da mujiya a wani fashi da makami, yayin da wasu barayi suka samu sabani bayan wata sata da suka yi, wanda hakan ne yasa su yakar juna inda suka bar gawawwakin biyu a wani sannannen wuri cikin Rukenya kusa da birnin Kutus a Kirinyaga dake kasar Kenya.

Kara karanta wannan

Karar kwana: Mutane 17 sun kone kurmus yayin da tankar mai ta kama da wuta

An tattaro yadda sama da 'yan fashi tara suka haura Thiba Falls Resort misalin karfe 3:00 na daren ranar Asabar, 19 ga watan Fabrairu, inda suka hanzarta yi wa mai gadin tsirara, gami da daure shi bayan sun nada mishi duka, shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Baya ga haka, sun balle wata mashaya, inda suka yi tatul da giya kafin su diba wasu su dora kan abun hawan da suka aje wajen harabar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng