An gano yadda fadar shugaban kasa ta bayar da gudumawar gaggawa wurin damke Abba Kyari
- Majiya daga fadar shugaban kasa ta sanar da yadda hukumar 'yan sanda ta yi kokarin kare Abba Kyari tare da kin mika shi gaban NDLEA
- An gano cewa kai tsaye Marwa ya nufa fadar shugaban kasa kafin ya samu sifeta janar kan batun harkallar kwayoyin Abba Kyari
- An dauka kwanaki bayan da Marwa ya samu sifeta janar kan batun amma hukumar ta ki bayar da Abba Kyari, hakan yasa NDLEA ta yi taron manema labarai ta fallasa
- Martanin jama'a daga fadin duniya ne yasa fadar shugaban kasa ta gaggauta kirar hukumar 'yan sanda tare da umartar ta da ta mika Kyari
Sabbin bayanai sun bayyana yadda aka damke fitaccen dan sanda, mataimakin kwamishinan 'yan sanda, Abba Kyari kuma aka mika shi ga hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi a makon da ya gabata.
Hukumar NDLEA ta bayyana cewa ta na neman Abba Kyari ido rufe, hakan ya zama dole ne bayan da hukumar 'yan sanda ta kasa ta cika umarnin NDLEA na bayar da Kyari domin amsa tuhuma, ThisDay ta ruwaito.
"Amma ganin kai tsaye fadar shugaban kasa ta shiga lamarin bayan taron manema labarai da NDLEA ta yi, hakan yasa aka gaggauta mika shi," wata majiya daga fadar shugaban kasa ta sanar.
Bayan shirya komai na tuhumar da ya hada da bidiyo, hotuna, sautin murya da hirar waya kan Abba Kyari da abokan harkarsa, NDLEA ta tattara tare da yi wa shugaban kasa bayani da sauran mutanen da ya dace su sani.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Bayan samun goyon bayan fadar shugaban kasan kan kama Kyari, hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyin ta tunkari sifeta janar na 'yan sanda.
Majiyar ta ce: "Shugaban NDLEA, Mohammed Buba Marwa, ya je kai tsaye inda yayi wa sifeta janar bayani, wanda bai san shugaban kasar ya san lamarin ba.
"An gabatar da hujjoji masu yawa da aka tattara kan Abba Kyari da yaransa inda aka bukaci da a saki Kayri ga hukumar kan binciken.
"Sifeta janar na 'yan sandan ya yi alkawarin za a mika Kyari a ranar Alhamis amma hakan bai faru ba. Juma'a ta iso ta kuma wuce babu abinda aka yi. Hukumar NDLEA ta dinga jira har cikin ranakun karshen mako amma shiru.
"Kyari wanda ya san abinda ke faruwa ya yi batan dabo. A daya bangaren ya dinga kiran mutanensa da ke fadar shugaban kasa domin su hana NDLEA kama shi."
ThisDay ta bayyana cewa, taron manema labarai da NDLEA ta shirya tamkar wani mataki ne da ta dauka bayan ta zargi hukumar 'yan sanda da kange Kyari da hukumarsu, wata majiya tace.
Majiya daga fadar shugaban kasa ta sanar da ThisDay cewa:
- "NDLEA ta samu bayanan sirri na cewa 'yan sanda na son sauya zancen ta hanyar mika wasu a matsayin wadanda ake zargi. Daga nan ne NDLEA ta gane cewa 'yan sanda suna son canza lamarin. Hakan ne yasa suka gaggauta yin taron manema labarai.
"Bayan kammala hira da manema labaran da kuma martanin jama'a daga fadin duniya, fadar shugaban kasa ta yi kira ga sifeta janar na 'yan sanda tare da umartar shi da ya mika Kyari gaban NDLEA a take. Daga nan ne masu kange Kyari a hukumar 'yan sanda suka san cewa lamarin ya kare dole ne a mika shi."
Yadda IGP da Marwa suka gana, suka shirya yadda za a damke Abba Kyari da mukarrabansa
A wani labari na daban, sabon labari ya bayyana a kan yadda sifeta janar na yan sanda, IGP Usman Alkali Baba da shugaban hukumar yaki da fasa-kwabrin miyagun kwayoyi (NDLEA), Birgediya janar Buba Marwa, suka hadu a hedkwatocin tsaro dake Abuja.
Sun yanke shawarar yadda za su bullo wa lamarin kwamandan hukumar binciken sirri na 'yan sanda da aka dakatar, DCP Abba Kyari, bisa hannunsa a harkallar safarar hodar iblis mai nauyin kilogram 25.
Bayanin yazo ne bayan kwana daya da 'yan sanda suka dakatar da duk wasu rassa na IRT na jihohin dake fadin kasar, wanda hakan ya biyo bayan kama DCP Kyari da aka yi.
Asali: Legit.ng