‘Yan bindiga sun ‘aure’ wasu yaran makarantar da aka gagara kubutarwa, sun yi masu ciki
- A watan Yunin 2021 ne aka ji labarin ‘yan bindiga sun yi awon-gaba da yaran makaranta a Yauri
- Har zuwa yanzu wasu daga cikin wadannan dalibai su na jeji duk da kuwa an biya kudin fansa
- Abin takaici, ‘yan bindiga sun aure wasu ‘yan matan, daga cikinsu har da wadanda aka yi wa ciki
Kebbi - Watanni takwas da dauke dalibai 80 daga makarantar sakandaren gwamnatin tarayya da ke Yauri, jihar Kebbi, har yanzu wasunsu ba su dawo ba.
Daily Trust ta kawo rahoto cewa duk da an biya kudin fansa ko an saki wasu ‘yan bindiga da ke tsare a gidan yari domin a fito da daliban, har yanzu shiru.
Rahoton da aka fitar a ranar 21 ga watan Fubrairu 2022 ya bayyana cewa akalla ‘yan mata 13 na wannan makaranta su na cigaba da zama a hannun miyagun.
Ana zargin ‘yan bindigan sun auri wadannan dalibai, har ma wasu daga cikinsu su na da juna-biyu.
Yaran Dogo Gide ne suka dura makarantar kwanar ta Yauri a jihar Kebbi a watan Yunin shekarar bara, suka yi awon-gaba da dalibai da kuma malamai biyar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jaridar ta ce yara 11 zuwa 14 ake zargin ‘yan bindigan su na cigaba da tsarewa, daya ne rak namiji, ragowar duk mata ne. Hakan ya bar iyayensu a cikin fargaba.
Bethel Baptist High School
A gefe guda kuma akwai wasu daliban makarantar Bethel Baptist High School a garin Kaduna da har yau suke tsare, watanni bakwai da suka wuce aka dauke su.
A shekarar bara ne ‘yan bindiga suka shigo wannan makaranta cikin duhun dare, suka sace yara da-dama, bayan sun hallaka wasu masu gadi da ke aiki a lokacin.
Wata majiya ta shaida cewa yara uku da aka ceto a watan Junairun bana, sun dawo wajen iyayensu dauke da cikin da ake zargin ‘yan bindigan su ka yi masu.
Mu na bakin kokarinmu - Gwamnati
Har yanzu akwai wasu yaran makarantun nan da ke hannun ‘yan bindigan da suka yi garkuwa da su. Kokarin kubutar da su ya ci tura duk da an fito da sauran.
Gwamnatin tarayya da ta jihar Kebbi sun bayyana cewa su na cigaba da kokarin ganin ragowar yaran da aka yi gaba da su, sun dawo gaban iyaye da ‘yanuwansu.
Yajin-aiki a makarantu
Ku na da labari cewa shiga yajin-aikin malaman jami'a a karkashin kungiyar ASUU ke da wuya, malaman FCE sun soma barazanar rufe makarantun kasar nan.
Kungiyar COEASU ta fara nuna alamun za a tafi yajin aiki a makarantun FCE idan har aka yi wasa. Malaman su na zargi gwamnati da saba masu alkawari.
Asali: Legit.ng