Jam'iyyar APC na shirya dage taron gangaminta zuwa watan Maris

Jam'iyyar APC na shirya dage taron gangaminta zuwa watan Maris

  • Majiyoyin daga cikin jam'iyyar APC sun bayyana cewa ana shirin dage taron gangaminta na kasa
  • A cewar majiyoyin, za'a gabatarwa shugaba Buhari wannan shawara idan ya dawo Najeriya daga Brussels
  • Mun kawo muku rahoton cewa Shugaba Buhari na kan hanyarsa ta dawowa da yammacin Asabar daga Belgium

FCT, Abuja - Da alamun taron gangamin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da aka shirya yi ranar 26 ga Febrairu, 2022, ba zai yiwu ba.

A cewar rahoton ThisDay, ana shirin dage taron gangamin da makonni biyu.

Duk da cewa jam'iyyar bata bayyana hakan ba, wata majiya tace shugabannin jam'iyyar da Gwamnoni zasu gaba da Shugaba Muhammadu Buhari don basa shawaran dage taron.

Ana kyautata zaton cewa rana 12 ga Maris za'a mayar.

Majiyar tace:

Kara karanta wannan

Mu ma nan ba da dadewa ba da yiwuwan mu shiga yajin aiki, Kungiyar Malaman Poly ASUP

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"An dage taron gangamin da makonni biyu amma ba'a sanar ba tukun. Kwamitin rikon kwarya da gwamnoni zasu gana da Shugaban kasa ranar Asabar (Yau) don bashi shawarar sabuwar rana."

Jam'iyyar APC na shirya dage taron gangaminta zuwa watan Maris
Jam'iyyar APC na shirya dage taron gangaminta zuwa watan Maris
Asali: Facebook

Hakazalika wani tsohon dan kwamitin gudanarwan jam'iyyar, wanda ya bukaci a sakaye sunansa yace ko shakka babu ba za'ayi taron ba.

Yace:

"Akwai abubuwan da ya kamata ayi kafin taron gangami ya yiwu ranar 26 ga Febrairu kuma ba'ayi hakan ba, ana saura 26 ga Febrairu."

Shugaba Buhari Ya dawo daga Brussels

Shugaba Muhammadu Buhari dawo gida Najeriya bayan tafiyarsa zuwa Belgium inda ya hallarci taron hadin kai na gamayyar kasashen Turai da gammayar kasashen Afrika karo na shida.

Hadimin Shugaba Muhammadu Buhari na yaa labarai gidajen rediyo da talabijin, Buhari Sallau, ne ya sanar da labarin tafiyarsa a shafinsa na Facebook.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng