Muna hanyar zuwa Kebbi daurin aure aka ce yan bindiga sun tare hanya, Shehu Sani
- Sanata Shehu Sani ya bayyana haln da suka shiga yayinda ska nufi jihar Kebbi halartan bikin daurin aure
- Dan siyasan wanda ke da niyyar takarar gwamnan Kaduna ya bayyana yadda suka kusa arangama da yan bindiga
- A cewarsa, yayinda wasu suka ce a cigaba da tafiyan, shi juyawa yayi
Tsohon Sanatan da ya wakilci Kaduna ta tsakiya a majalisar dokokin tarayya, Shehu Sani, ya bada labarin abin ya auku lokacin da suka dauki hanyar zuwa Kebbi halartan daurin aure.
Shehu Sani wanda ya shahara da yin jawaban barkwanci a kafafen ra'ayi da sada zumunta ya bayyana cewa an basu shawaran kawai suyi addu'a su cigaba da tafiyar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Shi kuwa bai bi wannan shawara ba, addu'a dai ya yi amma ya juya motarsa ya koma gida.
A sakon da ya daura shafinsa na Tuwita ranar Asabar, Shehu Sani yace:
"Muna hanyar zuwa Kebbi daurin aure, sai aka sanar da mu yan bindiga sun tare hanya."
"Wasu suka ce muyi addu'a su cigaba da tafiya. An yi addu'ar dani amma na juya na tafi gida."
Kaduna: Ina shirin aurar da 2 daga cikin 'ya'yana mata da aka sace, Basarake
A wani labarin kuwa, Malam Ibrahim Tanko, wani basarake a jihar Kaduna, wanda aka yi garkuwa da yaran shi mata guda hudu da matar shi, ya ce ana shirye-shiryen aurar da biyu daga cikin yaran a ranar 12 ga watan Maris na 2022.
Daily Trust ta ruwaito yadda a ranar Laraba, 'yan bindiga suka auka gidan Tanko, wanda shine Sarkin Hausawan Anguwar Azara cikin yankin Jere dake jihar Kaduna.
Tanko yayin zantawa da wakilin Daily Trust ta waya a ranar Asabar, ya bayyana yadda yake shirye-shiryen auran, yayin da 'yan bindiga suka kai musu farmaki.
Da aka tambaye shi ko sun kira sun nemi kudin fansa, ya ce 'yan bindigan sun tuntube shi a ranar Alhamis amma a kan wani abu daban.
Asali: Legit.ng