Taraba: Yan bindiga sun yi garkuwa da ɗan sarki da wasu mutum 7 a Arewa

Taraba: Yan bindiga sun yi garkuwa da ɗan sarki da wasu mutum 7 a Arewa

  • Mutum 8 cikinsu har da ɗan Hakimin yanki yan bindiga suka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Karim-Lamido a jihar Taraba
  • Wani mazaunin yankin yace mutane na cikin tashin hankali, domin yan bindiga na cin karen su babu babbaka rana da dare
  • Hakimin yankin Zip, ya tabbatar da sace ɗansa, kuma ya bayyana cewa sun nemi kudin fansa miliyan N70m

Taraba - Mutum takwas cikinsu har da ɗan Basarake yan bindiga suka sace a kauyen Illela, ƙaramar hukumar Karim - Lamido a jihar Taraba.

Daily Trust ta rahoto cewa yan ta'adda da suka kai adadin mutum 15 sun farmaki ƙauyen da misalin ƙarfe 4:00 na yammacin ranar Alhaamis.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan wani bangare ne daga cikin tawagar yan bindigan da suka addabi yankin a yan watanni kalilan da suka gabata.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: Yan bindiga sun kai kazamin hari, sun halaka mutane a jihar Benuwai

Yan bindiga a Taraba
Taraba: Yan bindiga sun yi garkuwa da ɗan sarki da wasu mutum 7 a Arewa Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Wani mazaunin yankin da abun ya faru, Dauda Suleiman, ya shaida wa yan jarida ta wayar salula cewa yan bindigan sun yi awon gaba da mutum 8 cikinsu har da dan Basaraken garin, sun tafi da su zuwa wurin da babu wanda ya sani.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wane hali mutanen yankin ke ciki?

Suleiman ya ƙara da cewa a halin yanzu yan bindiga ne ke da iko da yankin, suna yawo ɗauke da bindiga ba tare da wani yace musu uffan ba, da rana ko da dare.

A cewarsa babu wasu jami'an tsaro a ƙauyen, a koda yaushe mutane maza da mata na fama da fashi da kuma garkuwa.

Suleiman ya ce:

"Yanzun yan bindigan ke da ta cewa a yankin, sun tilasta wa mutane da dama barin gidajensu."

Shin yan bindigan sun nemi kuɗin fansa?

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi awon daga da dan Basarake a Abuja, sun bindige mutum daya

Hakimin Zip, Alhaji Uba, ya shaida wa manema labarai cewa ɗansa na cikin mutum takwas da maharan suka yi garkuwa da su, kuma sun nemi miliyan N70m kuɗin fansa.

Kakakin hukumar yan sanda reshen jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, bai ɗaga kiran wayar da aka masa ba balle jin ta bakin yan sanda.

A wani labarin na daban kuma kun ji cewa Amarya ta daba wa Uwar gida wuka har lahira mintuna kaɗan bayan Jima'i da Maigida

Wata Amarya ta yi ƙarfin hali ta caka wa uwar gida wuka har ta mutu saboda saɓanin kwanciyar aure da suka samu da Maigida.

Lamarin ya faru ne a jihar Ondo, kuma matar ta ce ba ta yi nufin kashe uwar gida ba, fushi ne kan abin da mijin ya mata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262