An kama wata mata mai shekaru 30 da ta ƙware wurin siyayya da jabun N1,000 a kasuwa
- Rundunar ‘yan sandan Jihar Ogun ta samu nasarar kama wata Bola Agbedimu mai shekaru 30 tana tsaka da kashe kudaden bogi a kasuwar Kila da ke karamar hukumar Odeda
- ‘Yan sanda sun kama ta ne bayan an kai korafin ta hedkwatar ‘yan sanda da ke Odeda kamar yadda DPO din yankin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Abimbola Ayeyemi ya shaida wa manema labarai
- A cewarsa, bayan bincike jakar ta, an ga N24,000 na kudaden bogin daga nan da bakinta ta shaida yadda take harkar kudaden bogin kuma take kashe su bayan cakuda su da masu kyau
Ogun - Rundunar ‘yan sandan Jihar Ogun ta kama wata mata mai shekaru 30, Bola Agbedimu bayan ta kashe kudaden bogi a kasuwar Kila da ke karamar hukumar Odeda a jihar, Daily Trust ta ruwaito.
Wacce ake zargin ta zo hannun hukuma bayan mutane sun kai korafin ta hedkwatar ‘yan sanda da ke Odeda akan kashe kudaden bogin a kasuwanni.
’Yan sanda sun yi gaggawar zuwa dan su damko ta
Vanguard ta bayyana yadda kakakin ‘yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi ya sanar da manema labarai a Abeokuta ranar Juma’a cewa an kai wa DPO din ofishin ‘yan sandan Odede, CSP Femi Olabode korafi, inda ya tura jami’an sa kasuwar daga nan suka yi ram da ita.
A cewarsa:
“Ana bincike jakar ta aka ga N24,000 na kudin bogin. Bayan ta sha tambayoyi, ta tabbatar da cewa tana harkar kudaden bogi.
“Ta ci gaba da bayyana cewa tana cakuda kudaden da masu kyau ne don ta yi siyayya.”
An sha kama ta a kasuwannin Abeokuta
Kakakin ya kara da cewa bincike na bayyana ba wannan bane karon farko, an dade ana kama ta a kasuwannin da ke Abeokuta.
Ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Lanre Bankole ya umarci a yi gaggawar mayar da ita bangaren binciken sirri daga nan a yanke mata hukunci daidai da abinda ta aikata.
Katsinsa: Ɗan Shekara 22 Ya Sace Wa Dattijuwa Kuɗinta Na Garatuti Baki Daya, Ya Siya Mota Da Babur
A wani labarin, Yan sanda a Jihar Katsina, a ranar Litinin sun yi holen wani Aliyu Abdullahi mai shekaru 22, mazaunin Kasuwar Mata Street a Karamar Hukumar Funtua saboda damfarar wata tsohuwa.
Ya wawushe mata dukkan kudinta na garatuti ta hanyar amfani da katin ta na banki wato ATM inda ya siya mota da babur da kudin, Vanguard ta ruwaito.
An taba kama mayaudarin, wanda ya kware wurin damfarar mutane ta hanyar sauya musu katinsu na ATM a baya amma daga bisani ya fito daga gidan yari kuma ya cigaba da laifin, rahoton Vanguard.
Asali: Legit.ng