Arziki na Allah: Dangote ya samu N2.49bn a cikin sa'o'i 24, ya ninka mai BUA sau 2

Arziki na Allah: Dangote ya samu N2.49bn a cikin sa'o'i 24, ya ninka mai BUA sau 2

  • Dangote ya kara samun makudan kudade duk da zarge-zargen da ake yi kan shirin haifar da karancin sukari ba gaira ba dalili
  • Kamfanonin Dangote Sugar Refinery Plc da Flour Mills of Nigeria Plc a wata budaddiyar wasika sun caccaki kamfanin BUA Foods da ya zarge su da dakatar da siyar da sukari
  • Yayin da ake ci gaba da wannan rikici, dukiyar Rabi’u a cikin sa’o’i 24 ta ragu da sama da Naira biliyan 12 a kasuwar hada-hadar kudi ta Najeriya

A 'yan kwanakin da suka gabata, kafafen yada labarai sun cika da labaran zargi da rikice-rikice tsakanin kamfanonin sukari na Dangote, BUA, da kuma Flour Mills kan haifar da karancin sukari.

BUA Foods a wani talla da aka buga a ranar Litinin ya ce Flour Mills ya dakatar da siyar da sukari saboda gwamnati ta ki amincewa da rabon sukari na 2022.

Kara karanta wannan

Yajin-aiki: Kafin magana ta yi nisa, Ministan ilmi na neman biyan bukatar kungiyar ASUU

Damgote ya kara arziki
Arziki na Allah: Dangote ya samu N2.49bn a cikin sa'o'i 24, ya ninka mai BUA sau 2 | Hoto: businessday.ng
Asali: Getty Images

Haka kuma ya zargi sukarin Dangote da dakatar da sayar da sukarinsa a wani yunkuri na haifar da karanci da kuma tilasta farashinsa a Najeriya.

Sai dai a wata sanarwar da aka buga a kan kasuwar hada-hadar kudi ta Najeriya a ranar Alhamis, kamfanin sukari na Dangote ya bayyana ikirarin da BUA ta yi a matsayin zunzurutun karya.

Sanarwar ta karyata zargen-zargen da kamfanin na BUA, inda tace hakan ba komai bane face kokarin bata kamfanonin tare da sanya BUA ta yi fice a kasuwa.

Hakazalika, sanarwar ta yi tsokaci kan yadda kamfanin BUA ya yi irin wannan ikirari daf da shiga Azumin Ramadana, wanda kuma hakan bai yiwa kamfanonin da suke gasa dadi ba.

Sanarwar ta kara da cewa:

"Mun yi imanin wannan halin da BUA ya nuna yana da ban tsoro kuma ya ci karo da ka'idojin gasar kasuwanci"

Kara karanta wannan

Hukumar kula da aikin 'yan sanda: Rahoton ’yan sanda game da Abba Kyari a cike yake da kura-kurai

Arzikin Dangote yana karuwa

Duk da tashe-tashen hankula da zarge-zagen da BUA ya yi, attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka ya ci gaba da tara dukiya yadda ba a tsammani.

Alkaluman da mujallar Forbes ta fitar sun nuna cewa arzikin Dangote ya karu cikin sa’o’i 24 da suka gabata da dala miliyan 6 (N2.49bn), kuma a halin yanzu shi ne na 143 mafi arziki a duniya.

Karuwar arzikin Dangote ya zo ne a daidai lokacin da kamfanin sa na sukari ya karu da 1.67% zuwa N18.3 daga N18 da ya buga harkalla a baya.

A daya bangaren kuma, dukiyar Rabiu ta tsaya a kan dala biliyan 6.9 ba tare da an samu wani sauyi ba.

Sabbin bayanai 4 game da Dangote da baku sani ba: Zai iya kashe N415m kullum na tsawon shekaru 40

A wani labarin, a shekara ta 11 a jere, hamshakin attajirin nan na Najeriya, Aliko Dangote, ya ci gaba da rike kambin lamba daya a jerin masu tarin kudi a nahiyar Afirka ba tare da fashi ko tsallake ba.

Kara karanta wannan

Ana ta bincike: Hukumar 'yan sanda ta dakatar da 2 daga cikin abokan harkallar Abba Kyari

Kamar yadda mujallar Forbes ta fitar a baya-bayan nan, karin 30% na farashin hannun jarin simintin Dangote wanda ya biyo bayan karuwar gine-ginen a Najeriya daga 'yan kasa da gwamnati ya ba da gudummawa ga karin dukiyarsa.

Legit.ng a bincikenta, ta kawo muku wasu sabbin abubuwa guda 4 masu ban sha'awa game da hamshakin attajirin wanda a halin yanzu dukiyarsa ta kai dala biliyan 13.9.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.