Babbar magana: Matar Aure ta maka mijinta a Kotu saboda ya ƙi amincewa sun yi aure
- Wata mata ta gurfanar da wani mutumi a gaban kotu kan yaƙi amincewa an ɗaura musu aure da jimawa a jihar Kaduna
- Mijin yace ya na da alaƙa da matar amma ta bariki, amma ba su kai ga auren juna ba kamar yadda ta yi ikirari
- Duk shaidun da aka gabatar a kotun sun ce alaƙa ce ta bariki, amma dai mutanen biyu ba su auri juna ba
Kaduna - Wata yar kasuwa, Khadija Muhammad, ta maka mijinta, Umar Abdullahi, a gaban kotun Shari'ar Musulunci dake Rigasa a Kaduna.
Daily Trust ta ruwaito cewa matar ta yi ƙarar maigidan ne saboda ya nuna sam bai aure ta ba, ba'a ɗaura musu aure ba.
Khadija ta shaida wa Kotu cewa ta aure shi, bayan ɗaura aure sai ya tafi ƙasar Saudi Arabiya, ta buƙaci Kotu ta taimaka wajen gano matsayin auren su.
Haka nan kuma matar ta shaida wa kotun cewa Mijinta ya karbi kayayyaki a wurinta na kimanin N194,300 tun 2017 amma har yanzu ya ƙi biyanta.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Shin ya amince da korafin matar?
Da yake kare kansa, wanda ake zargin ya musanta cewa ya Auri Khadija Muhammad, sai dai ya ce sun ɗan yi zaman bariki na wani lokaci amma ba aure ba.
Umar Abdullahi ya amince ta na bin shi bashin kuɗaɗe kamar yadda ta ambata, kuma ya shaida wa Kotu yana kokarin biyanta haƙƙinta.
Wane mataki Kotu ta ɗauka?
Hukumar dillancin labarai ta ƙasa, NAN ta rahoto cewa Alkalin kotun ya gayyaci shaidu domin tabbatar da auren mutanen biyu.
Amma baki ɗaya shaidun da aka gabatar a gaban Kotu ba wanda ya bayyana ƙarara cewa mutanen biyu sun yi aure, sai dai alaƙar bariki kawai.
Alƙalin Kotun, Mai Shari'a Malam Salisu Abubakar-Tureta, ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 9 ga watan Maris domin yanke hukunci.
A wani labarin kuma Daga karshe, Tsohon gwamna ya bayyana jam'iyyar da ya koma bayan ficewa daga PDP
Tsohon gwamnan jihar Ekiti , Segun Oni, yace ya shiga jam'iyyar SDP kuma zai nemi takarar gwamna a zaɓen 18 ga watan Yuni.
Oni ya sanar da cewa jiga-jigan manyan jam'iyyun APC da PDP na goyon bayan takararsa ta gwamnan Ekiti.
Asali: Legit.ng