Tashin Hankali: Wuta ta kama a dakin kwanan Dalibai suna tsaka da bacci, ta yi mummunan barna

Tashin Hankali: Wuta ta kama a dakin kwanan Dalibai suna tsaka da bacci, ta yi mummunan barna

  • Wata gobara da ta fara da tsakiyar dare ranar Laraba, ta yi ɓarna sosai a dakin kwanan ɗaliban wata makaranta a jihar Neja
  • Shugaban makarantar, Malam Muhammad Kontagora, ya ce jami'an hukumar kashe wuta na jihar Neja sun yi nasarar kashe wutar
  • Ya ce gobaran ta fara ne da ƙarfe 1:00 na daren ranar Laraba, lokacin da ɗalibai ke cikin bacci, amma babu wanda ya rasa rayuwarsa

Niger - Gobara ta tashi a ɗakin kwanan ɗalibai na kwalejin Musa Muhammad Kigera Science College dake sabuwar Bussa, ƙaramar hukumar Borgu, a jihar Neja.

Daily Trust ta rahoto cewa wutar ta kama a Hostel ɗin da tsakar dare, yayin da ɗaliban dake kwana a ciki ke bacci.

Gobara a Hostel
Tashin Hankali: Wuta ta kama a dakin kwanan Dalibai suna tsaka da bacci, ta yi mummunan barna Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Shugaban kwalejin, Malam Ibrahim Mohammed Kontagora, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai ta wayar salula.

Kara karanta wannan

Kotu ta sa a yi wa matashin ɗan kasuwa Bulala Bakwai a jihar Kaduna

Sai dai shugaban ya tabbatar da cewa tun daga farkon kamawar wutar zuwa sanalda aka yi nasarar kashe ta, ba bu wanda ya rasa rayuwarsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shin wace babbar ɓarna wutar da yi a Hostel ɗin?

A kalamansa yayin tabbatar da lamarin, shugaban kwalejin Malam Kontagora, ya ce:

"Baki ɗaya ginin gidan kwanan ɗaliban wanda ake kira 'Red House' ya kone, amma mun gode wa Allah ba bu wanda ya rasa rayuwarsa sanadin wutar."
"Sai dai kayayyakin dake cikin gidan waɗan da duke na ɗalibai ne da suka haɗa da kayan makaranta da sauran su, baki ɗaya sun kone."

Yaushe Gobarar ta fara ci?

Shugaban makarantar ya kara da cewa wutar ta fara ne da misalin ƙarfe 1:00 na dare lokacin dalibai na kwance suna bacci a ciki.

A cewarsa, daga bisani jami'an hukumar kashe Gobara na jihar Neja sun kawo ɗaukin gaggawa, kuma suka samu nasarar kashe wutar ba tare da ta tsallaka sauran gidajen kwanan ɗalibai ba.

Kara karanta wannan

Zamfara: Majalisa ta sake aike wa da zazzafan sako ga mataimakin Matawalle kan batun tsige shi

A wani labarin kuma Abba Kyari ya zargi kungiyar aware IPOB da kungiyar mayaƙanta ESN da kulla masa sharri dan ganin bayansa

A cewar mataimakin kwamishinan yan sandan da aka dakatar, sun sha alwashin bata masa suna saboda ya addabe su a kudu.

Kyari, wanda bai musanta saba wasu dokokin hukumar yan sanda ba, ya fuskanci fushin kwamitin kasancewar an masa gargaɗi kan aikata haka a baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262