Sheikh Guruntum ya yi wa'azi ga maza masu bin shafukan matan da ke raye-raye da nuna tsiraici

Sheikh Guruntum ya yi wa'azi ga maza masu bin shafukan matan da ke raye-raye da nuna tsiraici

  • Fitaccen malamin addinin Islama ya yi kira ga mutanen da ke yada bidiyon tsiraici da na 'yan matan soshiyal midiya suna rawar rashin da'a
  • Shehin ya bayyana cewa, Ubangiji ba ya son mutanen dake yada abubuwan ki a kafafan sada zumuntar zamani da yada alfasha
  • Ya kara da nuna yadda mai yada alfasha ke da kwatankwacin laifin mai aikata wa kuma Allah na iya jarabtar 'ya'yansa mata da muguwar dabi'ar

Fitaccen malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Guruntum, ya yi kira ga mutanen dake yada hotuna da bidiyon mata suna kwasar rawa, ko suna abubuwan da bai dace ba a kafafan sada zumuntar zamani, da su ji tsoron Allah su bar irin dabi'un nan.

Yayin maganar a bidiyon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Shehin ya ce, Ubangiji ba ya son mutanen da ke yada abubuwa marasa kyau a kafar sada zumuntar zamani ta hanyar yaba wa ko cigaba da wallafa irin abubuwan.

Kara karanta wannan

An maka dalibi mai shekaru 21 a kotu kan tura wa mijin budurwarsa hotunan tsiraicinta

Ku ji tsoron Allah: Sheikh Guruntum ya yi wa'azi mai ratsa zuciya ga masu yada alfasha a soshiyal midiya
Ku ji tsoron Allah: Sheikh Guruntum ya yi wa'azi mai ratsa zuciya ga masu yada alfasha a soshiyal midiya. Hoto daga darulfikr.com
Asali: UGC

Ya ce, Ubangiji ba ya kaunar irin dabi'un, kuma Ubangiji zai iya jarabtar 'ya'ya mata na mutum mai irin halin su dunga yada alfasha a kafafan sada zumuntar zamani.

"Ina shawartar mabiya mata masu nuna tsiraicin su a kafafan sada zumuntar zamani da wadanda ke bin shafukan da ba su dace ba a kafafan sada zumunci, da su ji tsoron Allah.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Allah ya na daukar duk mai hannu a yada munanan abubuwa da laifin kwatankwacin wanda ya aikata.
"Yarinyar ka ko 'yar uwarka ba ta kwasar rawa a kafar sada zumuntar zamani, amma kana nan kana bibiyar 'yar wasu da kannen wasu suna rawa a kafar sada zumunci.
"Hakan ya dace? Ba ku yi wa iyayen yaran da ku ke bi adalci ba. Kuma nuna yabawarka ga shafukan irin wadannan, ya na daga cikin yada alfasha a cikin al'umma.

Kara karanta wannan

Ni 'yar Drama ce, 'yar Nanaye, ina alfahari da hakan, Maryam Booth

"Da zarar ka nuna yabawarka ga wani abu da bai dace ba, kamar kana assasa yaduwar shi ne.
"Allah zai iya jarabtar ka ta hanyar sa yarinyar ka ta wallafa ababen da basu dace ba, kamar yadda wadannan yaran da ka ke bin su da yaba musu," Guruntum yace.

Akwai Abin Tsoro Da Takaici A Kasar Nan, Malamai dai sun yi nasu kokarin: Dr Rabiu Rijiyar Lemo

A wani labari na daban, babban Malamin addinin Islama kuma Lakcara a kwalejin ilimi dake Gumel a jihar Jigawa, Dr Rabiu Rijiyar Lemo ya yi tsokaci kan kisan gillan da ake yiwa yan Najeriya kulli yaumin.

Dr Rijiyar Lemo ya bayyana cewa ya zama wajibi Shugabanni su tashi tsaye wajen kare rayukan jama'arsu tare da hukunta masu aikata wannan laifi.

A jawabin da ya daura a shafinsa na Facebook, Malamin yace wadanda Allah ya daurawa hakkin jama'a su sauke hakkin da ke kansu.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya sun caccaki hadimin Buhari saboda rubutun da ya wallafa a Twitter

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng