Akwai Ire-Iren Abba Kyari a Cikin Rundunar 'Yan Sanda, AIG Iwar Mai Ritaya
- Mataimakin Sifeta Janar Na ‘Yan sanda mai ritaya, AIG Austin Iwar ya ce kamen Abba Kyari kan harkar miyagun kwayoyi yana nuna cewa akwai sauran jami’an ‘yan sanda masu irin laifukan shi
- Yayin tattaunawa da Channels TV a ranar Laraba, AIG Iwar ya ce batun dakatar da jami’in ‘yan sanda bisa zargin sa da FBI ta yi akan hada kai da Hushpuppi inda suka yi damfarar dala miliyan 1.1, yana nuna ya hada kai da wasu ‘yan sandan
- A shawarar da ya bayar ya ce ya kamata hukumar ‘yan sanda ta sallami DCP Abba Kyari kafin NDLEA ta kammala binciken ta, sannan ta tura sakamako ga bangaren hukunta ‘yan sanda kafin a yanke masa hukunci
Mataimakin sifeta janar na ‘yan sanda mai murabus, AIG Austin Iwar ya ce kama Abba Kyari akan harkar miyagun kwayoyi yana nuna cewa akwai ire-iren masu halayen sa a cikin jami’an ‘yan sanda ko kuma masu aikata laifukan da suka fi nashi muni, Vanguard ta ruwaito.
Yayin tattaunawa da Channels TV a wani shirin su na ‘Sunrise Daily’ na ranar Laraba, AIG Iwar ya ce batun dakatar da jami’in ‘yan sanda sakamakon shiga harkallar damfarar yanar gizo da Hushpuppi wanda FBI ta zarge shi da aikatawa, akwai yiwuwar ya ja hankalin wasu jami’an hukumar kuma ya bukaci su kare shi.
Yanzu hukumar ‘yan sanda ta ba NDLEA damar yin aikin da ya kamata ta yi kenan
Ya ci gaba da cewa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Dokar NPF da kundin tsarin mulki sun bayar da damar yin bincike akan laifuka ciki har da na harkokin miyagun kwayoyi. Batun cewa hukumar ‘yan sanda ta mika batun ga hukumar NDLEA don ta yi aikin ta ba tare da shiga ba na nuna cewa ‘yan sanda sun bar jami’an NDLEA su yi ayyukan da ya kamata ‘yan sanda su yi.
“In har ana so NDLEA ta yi aikin ta da kyau, wajibi ne hukumar ‘yan sanda ta sallami DCP Abba Kyari. Idan hukumar ta kammala binciken ta, sai ta tura wa ‘yan sanda don a mika ga kwamitin horarwar hukumar wacce zata sallame shi kafin a yanke masa hukunci.”
Gwamnati ba ta dauki ‘yan sanda da daraja ba
Vanguard ta nuna yadda AIG mai murabus din ya ci gaba da cewa:
“Gwamnati bata dauki hukumar ‘yan sanda da muhimmanci ba. Hukumar ce ya kamata ta yi aikin binciken amma ba a barinta ta yi ayyukan ta.
“Babu wani kudin da ake warewa na bincike ko kuma wasu ayyukan ‘yan sanda. Don haka ‘yan sanda ba su da wani zabi face su nemi kudin da zasu aiwatar da ayyukan su.”
Asali: Legit.ng