Kaduna: Kotu Ta Tura Kishiyoyi Zuwa Gidan Yari Saboda Fada Kan Mijinsu, Mijin Yace Akwai Yiwuwar Ya Sake Su

Kaduna: Kotu Ta Tura Kishiyoyi Zuwa Gidan Yari Saboda Fada Kan Mijinsu, Mijin Yace Akwai Yiwuwar Ya Sake Su

  • Wata kotun Shari'a da ke zamanta a Rigasa Kaduna ta bada umurnin a bawa wasu matan aure 2 masauki a gidan gyaran hali
  • Daya daga cikin matan ne ta yi shigar da kara a kotu cewa an mata duka kuma an cije ta, amma daga baya alkali ya gano fada suka yi kuma sun cije juna
  • Alkalin ya bada umurnin a tsare su na sati biyu a gidan gyaran hali don su koyi darasi kafin yanke hukunci, yayin da mijinsu ya ce akwai yiwuwar ya ake su

Jihar Kaduna - Wata kotun shari'a da ke zamanta a Rigasa, Jihar Kaduna ta tsare maan wani Danlami Tasiu a gidan gyaran hali tsawon sati biyu saboda fada ta cizon junansu a unguwar Bukuru.

Alkalin kotun, Salisu Abubakar-Tureta ya bada umurnin ne bayan ya gano matan biyu sun cije junansu a maimakon ikirarin da daya ta yi na cewa bata da laifi kuma ana musguna mata, rahoton Daily Nigerian.

Kara karanta wannan

Ta Musamman ce: Bidiyon yadda mata ta biya wa mijinta bashin N1.3m ya bar jama'a baki bude

Kaduna: Kotu ta tura kishiyoyi zuwa gidan yari saboda fada kan mijinsu, mijin yace akwai yiwuwar ya sake su
Kaduna: Alkalin kotun shari'a ya tura kishiyoyi 2 gidan gyaran hali saboda fada kan mijinsu. Hoto: The Cable
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mr Abubakar-Tureta ya ce an tsare su ne domin su samu damar yin tunani da nazari kan abin da suka aikata, ya kuma dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 28 ga watan Fabrairu.

Yadda abin ya faru

Daya daga cikin matan, Azima Usman Tasiu ce ta yi karar abokiyar zamanta a kotun kan zargin dukanta da cizonta.

Azima ta shaida wa kotun cewa ita ce matar Tasiu ta uku, ta kara da cewa an mata duka ne saboda karamin rashin jituwa da ya shiga tsakaninta da dan Aisha.

A cewar Azima, ranar girkinta ne ta tafi zuwa dibo ruwa daga rijiya, inda ta hadu da dan wanda aka yi karar. Ta umurci ya bari da diba ruwa amma ya ki.

Ta ce:

"Mahaifiyarsa ta zo ta tsinke gugar dibar ruwar ta tafi da shi dakinta.

Kara karanta wannan

Kano: Miyagu sun shiga har gida sun halaka matar aure, sun raunata 'ya'yanta 2

"Na bi ta domin in karbo; ina shiga dakinta, ta mare ni, ta fara duka na har da cizo."

Aisha, wacce ita ce matar Tasiu ta biyu, ta ce Azima ce ta fara kama ta da dambe bayan ta doki dan ta sannan ta duke ta ta kuma cije ta a kafada.

Alkali ya zurfafa bincike

Alkalin, wanda ya yi mamakin ikirarin da suka yi, ya bukaci su nuna masa bangaren jikinsu inda aka yi cizon kuma suka nuna masa.

Alkalin ya ce abin da ya faru fada suka yi ba wai mutum daya aka zalunta ba.

Shima, Tasiu, ya shaida wa kotun cewa ya tarar da su suna fada ya yi kokarin raba su amma bai yi nasara ba.

Mr Tasiu ya ce ko wane hukunci kotu ta yanke a ranar 28 ga watan Fabrairu, akwai yiwuwar zai saki dukkansu su biyun.

Kano: Mata ta garzaya kotun shari'a ta nemi a raba aurenta da mijinta saboda murguɗa baki

Kara karanta wannan

Ni 'yar Drama ce, 'yar Nanaye, ina alfahari da hakan, Maryam Booth

A wani labarin, mata ta maka mijin ta gaban kotu don bukatar a raba auren su sakamakon yadda rikici da tashin hankali ke aukuwa tsakanin su.

Ta bayyana gaban Alkali Munzali Tanko na kotun musulunci da ke zama a Kofar Kudu a birnin Kano don gabatar da korafin ta bisa ruwayar Dala FM.

Kamar yadda ta ce, mijin na ta ya na ci wa iyayen ta mutunci kuma ba ya ganin darajar su ko kadan kamar yadda ya zo a ruwayar na Dala FM.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: