Kwana 2 a Gamboru: Zulum da Shettima sun raba wa wadanda suka koma gida kudi da kayan abinci

Kwana 2 a Gamboru: Zulum da Shettima sun raba wa wadanda suka koma gida kudi da kayan abinci

  • Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno tare da Sanata Kashim Shettima sun ziyarci Gamboru inda suka kwashe kwanaki biyu
  • A ziyarar da suka kai sun rabawa 'yana gudun hijira da wadanda suka dawo daga gudun hijirar kudade da kayan abinci
  • Zulum ya samu rakiyar 'yar majalisa mai wakiltar, Ngala, Bama da Kala-Balge tare da kwamishinoninsa 3

Borno - Gwamnan jihar Borno, Frafesa Babagana Umara Zulum tare da Sanata Kashim Shettima sun ziyarci garin Gamboru da ke karamar hukumar Ngala daga ranar Lahadi zuwa Talata.

Shugabannin sun duba tare da shiga cikin masu raba kayan abinci da sauran kayan tallafi ga mutane 60,813 masu gudun hijira da wadanda suka koma yankin.

Zulum da Sanata Shettima sun yi tafiyar ne da motoci kuma a ranar farko ta tafiyar sun bai wa jama'ar yankin Gamboru da Ngala 55,253 kayan abinci da sauran kayan tallafi.

Kara karanta wannan

Borno: Gwamna Zulum na zawarcin likitoci ta hanyar inganta rayuwarsu a jiharsa, zai kara albashinsu

Kwana 2 a Gamboru: Zulum da Shettima sun raba wa wadanda suka koma gida kudi da kayan abinci
Kwana 2 a Gamboru: Zulum da Shettima sun raba wa wadanda suka koma gida kudi da kayan abinci. Hoto daga The Governor of Borno
Asali: UGC

Wadanda suka mori tallafin sun hada da mata 39,903 da suka samu tallafin N5,000 da zannuwa da maza 15,350 maza da suka samu tallafin shinkafa da masara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A rana ta biyu, wasu 'yan gudun hijira 5,560 da suka koma garin Wulgo da ke karamar hukumar Ngala duk an basu tallafi.

Daga cikinsu akwai mata 3,360 da suka samu tallafin kudi 5,000 kowacce da zani yayin da maza 2,200 suka samu tallafin buhunan shinkafa da na masara duk a Wulgo, kamar yadda wallafar gwamnan ta nuna a Facebook.

Zulum da Shettima sun yi tafiyar ne da 'yar majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Ngala, Bama da kala-Balge a tarayya, Dr Zainab Gimba, kwamishinoni Injiniya Mustafa Gubio, Injiniya Bukar Talba da Nuhu Clark tare da wasu jiga-jigan 'ya'yan jam'iyya mai mulki.

Wasu manyan masu ruwa da tsaki a karamar hukumar Ngala ne suka karba bakuncin Zulum da Shettima bayan isarsu yankin.

Kara karanta wannan

Buhari ya mika wa majalisa karin kasafin kudi, ciki har da na tallafin man fetur N2.557tr

Borno: Gwamna Zulum na zawarcin likitoci ta hanyar inganta rayuwarsu a jiharsa, zai kara albashinsu

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya yiwa likitoci da sauran ma’aikatan jinya alkawarin cewa gwamnatinsa za ta inganta jin dadinsu tare da duba albashi da ya dace da ayyukansu.

Zulum ya bayar da tabbacin ne a yayin ziyarar da suka kai garin Gamboru a karamar hukumar Ngala, tare da Sanata Kashim Shettima, inda suka kai kayan agaji daga ranar Lahadi zuwa Talata, Punch ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng