Idan NDLEA ta gama bincike kan Abba Kyari, za'a mika shi ga gwamnatin Amurka

Idan NDLEA ta gama bincike kan Abba Kyari, za'a mika shi ga gwamnatin Amurka

  • Bayan damke Abba Kyari da laifin safarar kwayoyi, da alamun gwamnati ta yanke shawarar mika shi ga Amurka
  • Wata majiya a fadar shugaban kasa ta bayyana cewa damke dan sandan da NDLEA tayi ya tabbatar da zargin da Amurka ke masa
  • Hukumar yan sanda ta damkawa NDLEA Abba Kyari tare da wani jami'an yan sanda dake aiki tare da shi

Majiyoyi a daren Litnin sun nuna cewa hukumar hana fasa kwabrin kwayoyi NDLEA na kammala bincikenta kan Abba Kyari, za'a mikashi ga gwamnatin Amurka.

TheNation ta ruwaito majiyoyin da cewa gwamnatin tarayya ta shirya da hukumar binciken Amurka FBI don mika mata Abba Kyari wanda take nema ruwa a jallo kan karban cin hanci hannun dan damfarar yanar gizo, Ramon Olorunwa Abbas Hushpuppi.

Kara karanta wannan

Sunayen abokan harkallar Kyari 2 da jami'an NDLEA dake da hannu a safarar miyagun kwayoyi

Majiya daga fadar shugaban kasa tace:

"Gwamnatin tarayya ta yanke shawarar mika Kyari ga Amurka idan NDLEA ta kammala bincikensa. Tuni ana tattaunawa tsakanin Najeriya da Amurka."
"Gwamnatin Amurka tuni ta aiko da takardun hujjoji ga gwamnatin tarayya. Tace akwai hujjar zargi kan Kyari. Yanzu damkeshi da akayi ya kara karfin hujjan Amurka."
"Abin karshe da ya rage shine rattafa hannu kan yarjejeniyar taimakekeniya dake tsakanin Najeriya da Amurka sannan a mika Kyari Amurka don bincike da hukunci."

Idan NDLEA ta gama bincike kan Abba Kyari, za'a mika shi ga gwamnatin Amurka
Idan NDLEA ta gama bincike kan Abba Kyari, za'a mika shi ga gwamnatin Amurka Hoto: Police IRT
Asali: Facebook

A baya mun kawo muku cewa Antoni Janar na tarayya, Abubakar Malami, ya bayyana cewa Gwamnatin Amurka da Najeriya na tattaunawa kan yiwuwan mika dakataccen jami'an dan sanda DCP Abba Kyari bisa zargin hannu cikin almundahanan $1m.

Abubakar Malami ya bayyana cewa lallai akwai kamshin gaskiya cikin tuhumar da ake yiwa Abba Kyari.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An mika Abba Kyari ga NDLEA bayan kamo shi da abokan harkallarsa

Malami ya bayyana hakan ne yayin hira a shirin 'Politics Today' na tashar ChannelsTV ranar Litinin.

Yadda Abba Kyari ya bamu cin hancin $61,400 don mu saki hodar Iblis 25kg, dilan kwaya ne: NDLEA

Hukumar hana fasa kwabrin kwayoyi a Najeriya tayi bayani filla-filla yadda ta gano dakataccen DCP na yan sandan, Abba Kyari, yana safarar kwayoyi.

Kakakin NDLEA, Femi Babafemi, a hira da manema labarai a Abuja ranar Litinin, ya ce Abba Kyari mamban kungiyar masu safarar kwayoyi daga Brazil zuwan Habasha zuwa Najeriya.

Babafemi yace Kyari ya tuntunbi wani jami'in hukumar a Junairun 2022 da a saki wasu hodar iblis da aka kama.

Karanta jawabin a nan

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng