Cikakken bayani: 'Yan sanda sun bi Abba Kyari da wasu mutane, sun kwamushe su

Cikakken bayani: 'Yan sanda sun bi Abba Kyari da wasu mutane, sun kwamushe su

  • Rahotannin da muke samu, sun bayyana cewa, an kama Abba Kyari da abokan harkallarsa mutum hudu
  • Wannan na zuwa ne bayan da wani bidiyo ya bayyana daga hukumar NDLEA inda Abba Kyari ke kulla harkalla
  • Hukumar ta ce tana nemansa ruwa a jallo, yanzu dai an kamo shi tare da mutanensa da suke aiki tare

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kama shugaban tawagar hukumar leken asiri ta IRT, DCP Abba Kyari da aka dakatar.

Jaridar Punch ta tattaro cewa, an kama shi ne tare da wasu mutane hudu ranar Litinin 14 ga watan Fabrairu.

Lokacin da Abba Kyari ke kokarin kulla harkallar miyagun kwayoyi
Aiki da cikawa: 'Yan sanda sun bi Abba Kyari da wasu mutane, sun kwamushe su | Hoto: tvcnews.tv
Asali: Twitter

An kama Kyari ne sa’o’i kadan bayan da hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa ta bayyana cewa tana neman sa bisa zargin alaka da safarar miyagun kwayoyi.

DCP Kyari da aka dakatar yana ci gaba da fuskantar bincike bayan da hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka ta tuhume shi da laifin harkallar damfara shi da Ramon Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppi.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An mika Abba Kyari ga NDLEA bayan kamo shi da abokan harkallarsa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jaridar TheCable ta ruwaito cewa, Olumuyiwa Adejobi, kakakin rundunar ‘yan sanda ne ya sanar da kama Kyari a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.

Adejobi ya ce, Usman Baba, sufeto-janar na ‘yan sandan Najeriya, ya bayar da umarnin kame Kyari tare da wasu jami’an ‘yan sanda hudu bisa zarginsu da hannu a safarar miyagun kwayoyi.

A cewar wani yankin sanarwar:

“Kamen jami’an ya biyo bayan bayanan da aka samu daga shugabancin hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) a ranar 10 ga watan Fabrairun 2022."

An mika Abba Kyari ga NDLEA bayan kamo shi da abokan harkallarsa

A yammacin nan, jami'in dan sandan da ake tuhuma da laifuka, DCP Abba Kyari, mataimakin kwamishinan ‘yan sandan da aka dakatar ya koma hannun hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) bayan kamo shi, TheCable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Jerin gaskiya 12 da baku sani ba game da ɗan sanda Abba Kyari da aka damke

A baya dai rundunar ‘yan sandan Najeriya ta sanar da cafke Kyari bisa zargin alaka da wata tawagar masu safarar miyagun kwayoyi ta duniya.

An dakatar da Abba Kyari a baya domin a binciki gaskiyar zargin da FBI ta Amurka ke masa na hannu a damfarar wani balarabe a kasar Qatar tare da Hushpuppi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.