Ta Musamman ce: Bidiyon yadda mata ta biya wa mijinta bashin N1.3m ya bar jama'a baki bude

Ta Musamman ce: Bidiyon yadda mata ta biya wa mijinta bashin N1.3m ya bar jama'a baki bude

  • Wasu gajerun bidiyoyi guda biyu sun nuna matakin da wani dan Najeriya ya dauka bayan da matarsa ta wanki kudinta har N1.3m ta biya masa bashi
  • Matar ta ce mijin nata ya kasance yana biyan kudaden da ya ci bashi tsawon shekaru duk wata kuma har yanzu bai gama biya ba
  • Lokacin da matar ta kira shi cikin dakin su don nuna masa cewa ta biya sauran bashin da ake binsa daga asusunta, sai kawai ya fashe da kuka tsabar murna

Wata mata ‘yar Najeriya ta shiga yanar gizo don nuna wasu faya-fayan bidiyon lokacin da ta sanar da mijinta cewa ta biya masa bashi.

Ta ce ba wai ta wanke shi daga bashin ne don ta yi alfahari da cewa tana da kudi ba sai don ta saukaka masa radadin rayuwa.

Kara karanta wannan

Kano: Miyagu sun shiga har gida sun halaka matar aure, sun raunata 'ya'yanta 2

Matar ta ce mijinta ya ari kudi ne a banki kimanin shekaru uku da suka gabata domin ya faranta wa iyalansa a gida.

Mata ta wanke mijinta daga bashi
Da kamar wuya: Bidiyon yadda mata ta biya wa mijinta bashin N1.3m ya bar baya da kura | Hoto: @mufasatundeednut
Asali: Instagram

A cewar matar, mutumin yana biyan kudin duk wata. Matar ta bayyana cewa lokacin da suka tafi kasar waje tare, ta yi tunanin za ta fara aiki nan take.

Ta kara da cewa ta dade tana fatan samun yadda zata warware masa wannan bashin.

A cewarta:

“Na yi tanadi ne saboda ina son sanya murmushi a fuskar mijina. Ina so in ga ya huta daga wannar damuwar.”

Lokacin da ta samu cikakken bayanin abin da ake bin mijinta nata, ta gano cewa har yanzu ana binsa Yuro 2,900 kwatankwacin N1,372,624.69 da zai biya. Matar ta biya duka kudin.

Bayan yin jawabi ga masu sauraronta, ta kira mijinta ta nuna masa abin da ta yi. Da mutumin yaga irin karimcin da ta yi masa, sai ya dauke ta har su biyun suka fadi kasa.

Kara karanta wannan

Ni 'yar Drama ce, 'yar Nanaye, ina alfahari da hakan, Maryam Booth

Mutumin nan take ya zauna a kasa ya fara rera wakar yabon ubangiji da yaren Igbo yana zabga kuka. Kai, abu dai sai wanda ya gani.

Kalli bidiyon farko:

Ga kuma na biyu nan:

A kasa mun tattaro muku martanin jama'a

do2dtun ya ce:

"Ba za ka taba fahimtar farin cikin mutum ba sai lokacin da ka dauke masa nauyi kuma wani lokacin kawai ka yi shi da farin ciki. Maza ba sakakwai bane."

paditaagu ya ce:

"Awwwwww. Wannan ta kowace hanya yana da kyau."

walejana ya ce:

"Aww wani abu ne mace ta yiwa namiji wani abu, wani abu ne kuma namiji ya yaba hakan kuma ya NUNA, wannan mutumin kirki ne."

Adesamh ya ce:

"Gaskiya ina ji wa wannan mutumin, farin cikinsa na gaskiya ne... babban mutum yana kuka."

onyeka3177 said:

"Chaiiii, soyayyar gaskiya tana da matukar muhimmanci a cikin aure."

mhyzprecious ya ce:

"Hawaye na kwaranya a kumatu na...soyayya abin mamaki."

Kara karanta wannan

Karon farko sun hau jirgi: Martani yayin da budurwa ta share wa iyayenta hawaye

Karon farko sun hau jirgi: Martani yayin da budurwa ta share wa iyayenta hawaye

A wani labarin, wata budurwa mai suna Mary Ogundimu ta shiga shafin LinkedIn domin bayyana yadda ta sakawa iyayenta farin ciki a fuskokinsu domin saka musu da irin sadaukarwa da suka mata a rayuwa.

Ta ce a karon farko cikin tsawon shekarun da suka yi a rayuwarsu, sun sami jin damar shiga jirgin sama, lamarin da ya faranta musu.

Mary ta ce ba ta damu da cewa mutane da yawa za su yi mamaki cewa ta yi wani babban al’amari na daukar nauyin tafiya ta jirgin sama ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Tags: