'Dan-karen wahalar mai ya sa farashin fetur ya tashi da kusan 150%, lita ta kai har N400

'Dan-karen wahalar mai ya sa farashin fetur ya tashi da kusan 150%, lita ta kai har N400

  • A halin yanzu, a kewayen birnin tarayya Abuja, samun man fetur ya zama tamkar samun wani gwal
  • Ana fama da dogayen layin mai tun bayan da gurbataccen man fetur ya shigo Najeriya daga ketare
  • Kamfanin NNPC ya kafa kwamiti na musamman domin ya kawo karshen matsalar da aka shiga

Mazauna Abuja da yankin jihohin Neja da Nasarawa su na fuskantar wahalhalu a sanadiyyar wahalar man fetur. Jaridar Punch ta fitar da wannan rahoto.

Rahoton da aka fitar a safiyar yau Litinin ya bayyana cewa har ta kai mutane su na sayen litar man fetur a kan N400 a hannun ‘yan bumburutu a halin yanzu.

Samun man fetur a birnin tarayya Abuja da kewaye sai a wajen ‘yan bumburutu a halin yanzu, wadanda suke saida mai a cikin robobi da ‘dan karen tsada.

Kara karanta wannan

Satar Abacha: Najeriya ta dauki Lauya, za tayi shari’a da kasar Birtaniya a kan €180m

A gidan man NNPC da ke titin Arab a Kubwa a garin Abuja, daruruwan motoci aka gani a kan layi. Hakan ya jawo aka samu mummunan cinkoso a kan hanya.

Haka zalika a gidan man Nipco da ke kan hanyar Abuja zuwa Zuba, akwai dinbin mutane da ke kan layin man, su na jira a iso kansu domin su iya zirga-zirga.

Man fetur
Layi a wani gidan mai Hoto: moovafrica.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A yankunan Nyanya da Mararrraba a jihar Nasarawa, babu wani gidan mai a bude a ranar Lahadi. Wannan ya sa ake fama da masifar wahalar mai a yankin.

Abin ya kai wasu jihohin

Legit.ng Hausa ta samu labari cewa lamarin ya kai jihar Kaduna, inda a wasu gidajen mai na Zariya wasu su na sayen lita tsakanin N195 zuwa N200 a gidan mai.

Wani rahoto na Katsina Post ya ce haka lamarin yake a Katsina, ta kai malamai sun fara magana.

Kara karanta wannan

Jonathan: Asalin abin da ya sa na kirkiro makarantun Almajirai a Arewa a mulkina

Hakan na zuwa ne kusan mako guda bayan an fara samun dogayen layi a gidajen mai a dalilin shigo da wani gurbataccen fetur da aka yi daga kasar waje.

A yi hakuri - NNPC

Da aka tuntubi NNPC, mai magana da yawun bakin kamfanin, Garba-Deen Muhammad ya ce mutane su kara yin hakuri, ba za a dade ba abubuwa za su lafa.

Dr. Garba-Deen Muhammad ya ce ma’aikatansu na iya kokarinsu na ganin an shawo kan lamarin, a cewarsa nan ba da jimawa ba za a nemi layukan a rasa.

NUPENG ta na barazana

Ku na sane cewa NNPC ta fitar da Biliyoyin kudi da za a gyara titunan da suka kwararrabe, NUPENG ta ce Gwamnoni da jami’an gwamnati na neman sace kudin.

Shugabannin NUPENG sun ce idan har aka nemi wadannan kudi aka rasa, za su tafi yajin-aikin da suka yi niyya kamar yadda suka fada a wata sanarwa jiya da yamma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng