'Karin Bayani: Yadda Jikan Sardauna, Magajin Garin Sokoto, Hassan Danbaba, Ya Rasu
- Alhaji Hassan Danbaba, jikan Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto, ya rasu a Kaduna yana da shekaru 51
- Danbaba, wanda shine shugaban masu nadin sarki a masarautar Sokoto ya yanke jiki ya fadi ne da rana a cewar rahotanni
- Ya rasu, kimanin shekara guda bayan rasuwar mahaifiyarsa, Aishatu, babban yar marigayi Firimiyan na Sokoto, Sir Ahmadu Bello
Kaduna - Magajin Garin Sokoto, Alhaji Hassan Danbaba, Shugaban masu nada sarki na masarautar Sokoto, ya riga mu gidan gaskiya.
Danbaba, ya yanke jiki ya fadi ne a otel dinsa a Kaduna misalin karfe 11.30 na safe. Ya rasu a hanyarsa ta zuwa asibiti a Kaduna, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Daily Trust ta rahoto cewa wani na kusa da iyalansa, Alhaji Buhari Sarkin Tudun Jabo, ya tabbatar da Danbaba ya rasu a Kaduna bayan gajeruwar rashin lafiya.
Ya shaida wa Daily Trust cewa:
"Muna cikin kaduwa, don haka ba zan iya baka cikakken bayani ba a yanzu. Muna shirin kai gawar mamacin ne zuwa Sokoto inda za a masa jana'iza.
"Za a birne shi a garinsu a Sokoto a yau. Wannan babban rashi ne ba kawai ga iyalansa da Jihar Sokoto ba, amma rashi ne ga kasa baki daya."
Yadda Magajin Garin Sokoto ya rasu
Wata majiyar daban ta ce:
"Magajin ya zo Kaduna ne ranar Alhamis domin ya jajantawa Ministan Tsaro, Janar Aliyu Gusau, bisa rasuwar dan uwansa.
"Kamar yadda ya saba, ya sauka a otel dinsa, Stonehedge a birnin Kaduna.
"Gusau da Magajin sun yi shirin su bar Kaduna tare su tafi Abuja a ranar Asabar. Bayan ya yi wanka misalin karfe 11 na safe. Ya saka kaya domin ya tafi wurin Janar Gusau a gidansa.
"Muna shirin tafiya, ya yanke jiki ya fadi. Hadimansa suka taru suka dauke shi suka kama hanyar asibiti nan take. Amma, a hanya sai ya ce ga garinku."
Magajin Garin na cikin manyan yan Najeriya da suka hadu a Legas a makon da ta gabata domin tattaunawa kan yadda za a kawo karshen matsalolin Najeriya gabanin 2023.
Kafin rasuwarsa, Magajin Garin shine Direktan Jaridar THISDAY.
A dakaci karin bayani ...
Asali: Legit.ng