Na so yin shuhura da sunan karuwa a Twitter, Sabuwar Salma ta Kwana Casa'in

Na so yin shuhura da sunan karuwa a Twitter, Sabuwar Salma ta Kwana Casa'in

  • Jarumar da ta fito a sabuwar Salma a shirin Kwana Casa'in, Mufeeda, ta bayyana yadda ta so shahara a Twitter da sunan karuwa
  • A cewar Mufeeda, ta san idan ta yi amfani da hashtag wato likau mai sunan Ashawo, babu shakka za ta shahara kuma zata zama abun magana
  • Amma kuma ta ce ta fasa ne ganin cewa ita 'yar arewa ce kuma babu shakka ta shiga uku idan ta yi amfani da wannan likau dina

Sabuwar Salma ta shirin Kwana Casa'in ta sanar da dalilin da ya hana ta shahara a dandalin sada zumunta na Twitter wanda ta bayyana shafin ta na Instagram.

A wata wallafar bidiyo da ta yi, ta yi bayani cikin harshen turanci.

Na so yin shuhura da sunan karuwa a Twitter, Sabuwar Salma ta Kwana Casa'in
Na so yin shuhura da sunan karuwa a Twitter, Sabuwar Salma ta Kwana Casa'in. Hotuna daga @princess_mufeedah
Asali: Instagram

A bayanin sabuwar Salma, ta ce tun bayan dawowar Twitter a Najeriya ta ga yadda ake shiga jerin batutuwa wadanda suka fi shahara da ake tattaunawa a dandalin wato trending news.

Kara karanta wannan

Alheri danko: Wata kungiyar musulunci ta kawo alheri Kaduna, ta yi aikin jinyar ido kyauta

Cikin kankanin lokaci za ka iya samun masu sake wallafa hotuna ko batutuwan ka a dandalin, hakan yasa ta so amfani da wani likau, wanda ake kira da Hashtag na Ashawo wanda karuwa ya ke nufi a jikin hotunan ta da rubutun ta.

Ta kara da cewa:

"Na tuna daga yankin arewa nake shiyasa na hakura don a zauna lafiya. Shiyasa na kasa amfani da likau din wanda da na yi amfanin da shi ranar da tawa ta kare."

Me masu tsokaci suka ce?

Nan take jama'a suka yi caa a kan sabuwar Salman inda suka ce gara da ta fasa dan kuwa sai an yi maganar.

Wadanda ba Hausawa ba 'yan arewa sun dinga kushe wannan abu da suka kira da rashin 'yanci yayin da Hausawa suka dinga soka wa jarumar maganganu marasa dadi.

Kara karanta wannan

Surukata ce ta hure wa matata kunne, Magidanci da ke neman kotu ta datse igiyar aurensa

Bidiyon jarumar ya tabbatar da cewa, ba don tsoron cece-kuce a shafukan sada zumunta ba, da wani abun ido ba zai iya kallo ba.

Ga bidiyon jarumar:

Sabbin hotunan Rahama Sadau da Hadiza Gabon sun janyo cece-kuce

A wani labari na daban, sabbin hotunan jaruman Kannywood, Rahama Sadau da na Hadiza Aliyu Gabon sun janyo maganganu daban-daban a kafar sada zumuntar zamani ta Instagram.

A kwanaki biyu da suka gabata, jaruma Rahama Sadau ta wallafa wasu hotunan ta sanye da wata bakar riga wacce ke bayyana ilahirin surar jikin ta.

Kamar yadda ta wallafa a shafin ta mai suna @rahamasadau, ta saka hotunan tare da rubuta:

"Ba za ka taba gajiya ba matukar ka na gwada sabbin abubuwa".

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng