Bayan shekaru 18 da rasuwar Balaraba, Jarumi Shu'aibu Lawan Kumurci ya sake aure
- Fitaccen jarumin masana'antar Kannywood, Shu'aibu Lawan wanda aka fi sani da Kumurci ya angwance da zukekiyar amarya
- A hotunan da Ahmed Gandujiyya ya wallafa a shafinsa ya ce Kumurci ya taba auren wata ta rasu bayan Balaraba
- Allah ya yi wa tsohuwar matarsa Balaraba rasuwa ne bayan da aka daura aurensu kuma ana kan hanyar kai ta dakin angonta Kumurci
Bayan kusan shekaru ashirin da rasuwar rabin ransa, jaruma Balaraba Muhammad, jarumi Shu'aibu Lawan wanda aka fi sani da Kumurci ya sake angwancewa.
Wani ma'abocin amfani da kafar sada zumunta ta Facebook mai suna Ahmed Prince Gandujiyya ya wallafa hotunan a shafinsa.
Gandujiyya ya shaida cewa Kumurci ya taba wani auren bayan jaruma Balaraba ta rasu amma Allah ya yi wa sabuwar amaryar rasuwa.
Kamar yadda gandujiyya ya sanar:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Ango Sha'aibu Lawan (Kumurci) ya yi sabon aure tun bayan shekaru 18 da rasuwar Matar sa Balaraba.
"Amma wasu rahotannin sun yi nuni da ya taba yin aure bayan rasuwar marigayiya Balaraba ya auri Maryam Umar ita ma ta rasu. Allah ya sanya Alheri."
'Yan matan Kannywood 4 da suka rasu da kuruciyarsu
A wani labari na daban, daya daga cikin babban abu a duniyar nan mai girgiza zukatan jama'a shine mutuwa, duk da kuwa an san dole ne kowa ya dandanata.
Babu shakka mutuwa dole ce, tunda Allah ne ya tabbatar da cewa kowacce rai sai ta dandana zafinta.
Masana'antar fina-finan Hausa wacce aka fi sani da Kannywood, ta dandana rashe-rashe da dama. Daga ciki kuwa akwai na 'yan matan masana'antar wadanda suka shahara.
Bayan shekaru 49, shahararren mai neman shugabancin kasa na PDP ya ziyarci garinsu da sunan zai tsaya takara
Ga wasu daga cikin 'yan matan masana'antar da suka rasa rayukansu da kananan shekarunsu:
1. Fadila Muhammad: Fitacciyar jarumar masana'antar fina-finan hausa wacce ta yi sharafi daga shekarar 2011 zuwa 2014, ta rasu a ranar 29 ga watan Augustan 2020 bayan gajeriyar rashin lafiya. Tana daya daga cikin jarumai masu matukar salo da farin jini a masana'antar.
Matashiyar jarumar tana da wani irin salo na bayyana a wasan kwaikwayo, wanda ke saka zukatan masu kallo cikin nishadi. Tauraruwarta ta fara haskawa tun bayan da ta fito a fina-finai masu suna Hubbi da Basaja.
Babu shakka wadannan fina-finan sun saka sunanta ya dauku ga ma'abota kallon fina-finan Hausa. Babu shakka za a ci gaba da tunawa da ita matukar za a ambaci tarihin masana'antar fina-finan. Ta rasu tana da shekaru 27 a duniya.
Asali: Legit.ng