Karin bayani: Kotu ta yi watsi da karar N66bn da gwamnoni suka shigar a kan gwamnatin Buhari
- Kotun koli ta yi watsi da Dokar Zartaswa ta 10 (E010) da ke neman samar da kudaden tafiyar da hukumomin shari'a da majalisar dokoki a jihohi
- Kotun koli ta ce dokar ta saba da kundin tsarin mulkin Najeriya, don haka ta ajiye dokar a gefe ba tare da wata-wata ba
FCT, Abuja - Kotun koli ta bayyana Dokar Zartaswa ta 10 (EO10) da ke magana kan samar da kudaden tafiyar da Hukumar Shari'a da Majalisar Dokoki ta Jihohi a matsayin haramtacciyar doka kuma wacce ta sabawa kundin tsarin mulki, inji rahoton Channels Tv.
Kotun kolin ta kuma yi watsi da karar Naira biliyan 66 da gwamnonin jihohi suka shigar a kan gwamnatin tarayya.
A hukuncin da aka fitar ranar Juma'a, mafi rinjayen kwamitin mutane bakwai na kotun sun amince cewa shugaban kasa ya zarce ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi wajen bayar da dokar ta EO10.
Shida daga cikin bakwai na kwamitin sun yi watsi da batun inda suka ajiye tare da yin watsi da takardar EO10 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Hukuncin ya kuma bayyana cewa, ba alhakin gwamnatin tarayya ba ne ta samar da kudaden tafiyar da aiki da kuma na kashewa akai-akai na manyan kotuna da aka kafa wa Jihohi a karkashin sashe na shida na kundin tsarin mulki.
Dukkan mambobin bakwai sun amince cewa Jihohi ba su da ikon a mayar musu da duk abin da suka kashe a baya don kula da wadancan kotunan.
Hukuncin ya zo ne a kan karar da Jihohi 36 suka shigar a kan FG kan kudade na bangaren shari’a da kuma tsarin mulki na EO10.
Gwamnoni suna fake wa da Buhari domin ɓoye rashin kwazon su, Femi Adesina
A wani labarin, mai ba wa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawarwari na musamman, Femi Adesina ya zargi wasu gwamnoni da fake wa da Buhari wurin boye rashin kwazon su, The Punch ta ruwaito.
A wata wallafa wacce Adesina ya saki a shafinsa na Facebook ranar Alhamis, mai taken, ‘Zulum Zooms In’ ya kula da yadda gwamnonin suke mayar da laifi akan Buhari ko da suna da hannu a ciki.
Ya ce shugaban kasa a sake yake da kowa har da masu caccakarsa cikin gwamnonin amma duk da hakan sun zabi mayar da suka akan sa.
Asali: Legit.ng