An bindige Ladani har lahira yana tsaka da kiran sallar Asubahi a Zamafara

An bindige Ladani har lahira yana tsaka da kiran sallar Asubahi a Zamafara

  • Wasu yan bindiga marasa imani sun harbe Ladan har lahira yayin da yake cikin kiran Sallah ta Asubah a jihar Zamfara
  • Rahoto ya nuna cewa Ladanin na cikin Masallaci yana kiran Sallah lokacin da yan ta'adda suka shigo kauyen Mazagu, suka kashe shi
  • Tun bayan tsintar gawar wani ɗan bindiga a bayan kauyen, yan ta'adda suka hana mutanen yankin sakat

Zamfara - Yan bindiga sun kashe wani Ladani yayin da yake cikin kiran sallar Asuba a ƙauyen Magazu, dake karamar hukumar Tsafe, a jihar Zamfara.

Mazauna ƙauyen sun shaida wa wakilin jaridar Daily Trust cewa Ladanin ya na cikin Masallaci yana kiran Sallah lokacin da yan bindigan suka shigo kuma suka harbe shi har ya rasu.

Taswirar jihar Zamfara
An bindige Ladani har lahira yana tsaka da kiran sallar Asubahi a Zamfara Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Ƙauyen Magazu, na da nisan kilomita 40 daga ɓangaren kudancin Gusau, babban birnin jihar Zamfara, kuma yana kan hanyar Gusau zuwa Funtua ta jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama hatsabibin yaro na hannun daman kasurgumin ɗan bindiga a Zamfara

Tun bayan tsintar gawar wani ɗan bindiga a bayan gari kwanan nan, yan ta'addan suka jefa kauyen cikin halin rashin tabbas da zaman ɗar-ɗar.

Bayan haka ne, yan ta'adda suka sha alwashin ɗaukar fansar ɗan uwansu da aka kashe, wanda suka ɗora laifin kan mazauna ƙauyen Magazu.

Wace ɓarna suka yi yayin harin?

A harin da suka kai ranar Laraba, yan bindigan sun yi garkuwa da mutum ɗaya. kuma ba tare da ɓata lokaci ba suka bukaci a tattara musu miliyan N7m kuɗin fansa.

Wani mazaunin yankin ya shaida mana cewa, "Ba mu ne muka kashe ɗan uwan su ba kamar yadda suke zargi."

Rahotanni sun bayyana cewa yan bindiga wanda yanzu aka ayyana su a matsayin yan ta'adda sun saka ƙauyen Magazu a gaba duk da jami'an tsaron dake yankin.

Kara karanta wannan

Nasara: Jiragen yakin Najeriya sun kashe shugabannin yan bindiga da yaransu 37 a Neja

Har zuwa yanzun da muka haɗa wannan rahoton, babu wata sanarwa a hukumance daga hukumar yan sanda reshen jihar Zamfara kan lamarin.

A wani labarin kuma Gwamnan PDP dake son gaje Buhari ya shiga Katsina, ya jero matsalolin da za'a shiga idan APC ta zarce

Gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal, ya kai ziyara jihar Katsina a cigaba da neman shawara da goyon baya kan takararsa a 2023.

Tambuwal yace matukar yan Najeriya suka sake APC ta zarce kan madafun iko, tattalin arziƙi da tsaro zasu kara lalacewa a faɗin kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262