Katsina: Tirela ta murƙushe fasinjoji 10 da shanu 30, sun halaka har lahira

Katsina: Tirela ta murƙushe fasinjoji 10 da shanu 30, sun halaka har lahira

  • Wata tirela dauke da shanu da fasinjoji wacce ta doshi kudu ta kubce a wani kauye a jihar Katsina, shanu talatin sun mutu
  • Ganau ya shaida wa manema labarai yadda tirelar tayi tintsira gudi-gudi a tsakiyar daren Alhamis inda ta kashe fasinjoji goma
  • Sai dai daya daga cikin wadanda iftila'in ya fada musu ya ce, kusan dukkan wadanda suka yi hatsarin daga karamar hukumar Malumfashi suke

Katsina - A safiyar Alhamis, 10 ga watan Fabrairun shekarar 2022, wata tirela dauke da shanu da fasinjoji wadda ta doshi kudu daga Katsina ta kubce a kauyen Gora a karamar hukumar Malumfashi dake jihar Katsina.

Lamarin ya yi sanadiyyar halakar a kalla fasinjoji 10, shanu 30, inda mutane da dama suka samu raunuka, Vanguard ta ruwaito.

Katsina: Tirela ta murƙushe fasinjoji 10 da shanu 30, sun halaka har lahira
Katsina: Tirela ta murƙushe fasinjoji 10 da shanu 30, sun halaka har lahira. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Ganau daga yankin mai suna Mallam Bilya wanda ya zanta da Vanguard ya ce:

Kara karanta wannan

Almundahanar kudin makamai N13.8bn: An hana tsohon shugaban Soji fita kasar waje

"Tirelar dake dauke da shanu da fasinjoji wacce ta taso daga Dankama a karamar hukumar Kaitan jihar Katsina wacce ta nufi Warri dake jihar Delta, ta kubce a kauyen Gora, inda ta yi tintsira gudi-gudi tsakanin karfe 12:00 zuwa 1:00 na safiyar Alhamis."

Kamar yadda mutum dayan daga cikin wadanda suka rayu cikin wadanda al'amarin ya ritsa dasu ya bayyana, wanda a halin yanzu yake samun kulawa a babban asibitin Malumfashi ya ce:

"Kusan dukkan wadanda suka yi hatsarin daga karamar hukumar Kaita dake jihar Katsina suke, amma an sheda wa iyalan su."

Yayin da aka tuntubi kakakin hukumar kula da hadarurruka tare da kai kawon ababen hawa a jihar, Abubakar Usman ya ce:

"Motar kadai hatsarin ya shafa, kuma ya auku ne misalin karfe 12:10 na safiyar ranar Alhamis a gundumar Gora dake karamar hukumar Malumfashi.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Mota dauke da silindar gas ta fadi a Kano, ta lalata kayayyaki, ta yi kisa

"Lamarin ya faru ne da wata tirela mai dauke da lambar rigistar KTN 495 XA, dankare da dabbobi da fasinjoji, wacce ta nufi kudancin Najeriya, yayin da ta kubce a wani lungu ta kifa.
"Har yanzu ba mu tabbatar da yawan mutanen da suka rasa rayukan su ba, amma kamar yadda ganau da yaran mu da suka kai dauki suka ce, sun ga matattun shanaye 30."
Game da yawan fasinjojin da suka rasa rayukan su, kakakin FRSC ya ce, "a halin yanzu, tawagar binciken mu tana wurin, muna jiran rahoto kuma za mu sanar da ku daga baya."

Jirgin ƙasa ya markaɗe tirelar siminti da adaidaita sahu a Kano

A wani labari na daban, jirgin ƙasa dauke da fasinjoji ya markaɗe tirelar siminti da kuma adaidaita sahu wacce aka fi sani da Keke Napep a Kano.

Mummunan al'amarin ya auku ne a titin Obasanjo da ke ƙwaryar birnin Kano a safiyar Lahadi, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kaduna: Jami'an tsaro sun ragargaji 'yan bindiga, sun kubutar da wadanda aka sace

Ganau ba jiyau ba waɗanda ke kasuwanci a kusa da layin dogon, ya ce sun ga tirela ta na tafe kusa da dogon yayin da jirgin ƙasan ya dumfaro wurin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: