Gwamnoni da Majalisar Tarayya na neman taba karin albashin da aka yi ta bayan-fage

Gwamnoni da Majalisar Tarayya na neman taba karin albashin da aka yi ta bayan-fage

  • ‘Yan Majalisa sun kuma farfado da kudirin da zai kawo sauyi a tsarin mafi karancin albashi a Najeriya
  • Hon. Garba Datti Muhammed ya kawo kudirin da zai bada ‘yanci wajen yanke albashin ma’aikata
  • Kamar maganar ta mutu saboda adawar ma’aikata, ‘yan majalisar wakilan tarayya sun sake tado ta

Abuja - Akwai kokarin da ake yi a majalisar wakilan tarayya na yi wa tsarin mulkin Najeriya garambawul domin a kawo sauyi a mafi karancin albashi.

Jaridar Vanguard ta ce wanda ya dauko wannan aiki shi ne ‘dan majalisar Sabon Gari, jihar Kaduna a majalisar tarayya, Hon. Garba Datti Muhammed.

Honarabul Datti Muhammed ya na so a cire nauyin tsara mafi karancin albashi daga wuyan gwamnatin tarayya, a ba gwamnoni ikon su samu ta-cewa.

Wannan yunkuri na ‘dan majalisar ya gamu da bakin jini a wajen ma’aikata. Ana zargin majalisar wakilai ta bijiro da wannan kudirin ne saboda manufarta.

Kara karanta wannan

Satar Abacha: Najeriya ta dauki Lauya, za tayi shari’a da kasar Birtaniya a kan €180m

Kungiyoyin kwadago, ‘yan kasuwa da sauran wasu masu zaman kansu duk sun nuna ba su goyon bayan wannan kudiri da suke gani zai cuci ma’aikata.

'Yan Majalisar Tarayya
Hon. Garba Datti Muhammed da 'yan kwamitinsa a Majalisa Hoto: nigerianports.gov.ng
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ganin an matsa a 2021, dole ta sa ‘yan majalisa suka jinginar da kudirin na Hon. Muhammed a gefe. Labarin da muke samu shi ne an lallabo da maganar.

Wata majiya ta shaidawa jaridar cewa gwamnoni da sauran wadanda suke goyon bayan kudirin ba su hakura ba, su na ta kokarin ganin ya samu karbuwa.

Dama can kudirin ya tsallake matakin sauraro na biyu a majalisar wakilai kafin ayi shiru da maganar.

Bincike ya nuna cewa gwamnonin jihohi za su san yadda za a yi a farfado da kudirin, a san yadda za ayi wajen ganin majalisa ta amince da kwaskwarimar.

Idan kudirin ya zama doka, zai zamana gwamnoni da shugaban kasa duk su na da ‘yancin da za su yanke mafi karancin albashin da za su biya ma’aikatansu.

Kara karanta wannan

Ronaldo, Ozil, Mane da sauran ‘Yan kwallon kafa da suka fi kowa taimakawa marasa karfi

Anyim Pius Anyim a 2023

A makon nan ne aka kawo rahoto cewa ‘Ya 'yan PDP a Majalisa sun tsaida wanda suke goyon baya ya nemi takarar Shugaban kasa a jam'iyyarsu a 2023.

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya yana kara karfi sannu a hankali a PDP bayan an ji cewa marasa rinjayen na goyon bayan a ba Anyim Pius Anyim tuta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng