Hanifa: Abdulmalik Tanko da sauran wadanda ake zargi sun samu lauya
- Antoni janar na jihar Kano, Barisat Musa Abdullahi Lawan ya sanar da cewa Abdulmalik Tanko da mutum 2 da ake zargi da kisan Hanifa sun samu lauya
- Kamar yadda kwamishinan shari'ar na jihar Kano ya bayyana, Majalisar Taimako ta Shari'a a Najeriya ta bayyana cewa za ta tsaya musu
- Hakkin dan Adam ne a Najeriya, duk wanda ake zargi da kisan kai da ya samar da lauya ko kuma gwamnatin jiharsa ta samar masa
Kano - Antoni janar na jihar Kano kuma kwamishinan shari'a, Barista Musa Abdullahi Lawan, ya bayyana cewa Majalisar taimako ta sharia'a ta Najeriya ta bayyana bukatar ta wakiltar Abdulmalik Tanko da sauran wadanda ake zarginsu da kisan yarinya mai shekaru biyar, Hanifa Abubakar.
Antoni janar din ya sanar da Daily Trust a ranar Alhamis cewa, wannan ya biyo bayan umarnin Mai shari'a Usman Na'abba na babbar kotun jihar Kano ne a ranar 5 ga watan Fabrairu inda ya ce jihar ta samarwa da Tanko da sauran mutum biyun lauya.

Kara karanta wannan
Kisan Hanifa Abubakar: Gwamnatin Ganduje zata baiwa Abdulmalik Tanko Lauyan da zai kare shi

Source: Twitter
Lawan ya ce duk wanda ke fuskantar shari'a kan zargin kisan kai, ana bukatar ya samu lauya kuma idan mutum ba shi da lauya sannan ba shi da halin samowa, gwamnatin tarayya ta bukaci jiharsa da ta samar masa.
Ya yi bayanin cewa Majalisar shari'ar ta Najeriya kafuwar gwamnatin tarayya ce wanda aikinsu ya kama da samar da lauya kyauta ga duk dan Najeriyan da bashi da lauya kuma ake zarginsa da kisan kai wanda hukuncinsa kai tsaye na kisa ne.
"Tawagar lauyoyinmu a shirye suke da su gabatar da gamsassun shaidu kan Abdulmalik Tanko da sauran mutane biyun, amma ba zai yuwu a cigaba ba. Idan muka samu aka yanke hukunci a kansu ba tare da lauya ba, babu shakka za a soke shari'ar idan aka daukaka kara," yace.

Kara karanta wannan
'Yancin mata ne: Gwamnatin Buhari ta magantu kan batun hana sanya Hijabi a makarantun Kwara
Ya bayyana cewa, ba wai daga kasar bane kawai har da hakkin dan Adam na samun wakilci a duk abinda ya hada da lamarin kisan kai.
Ana zargin Tanko da wasu mutum biyu da garkuwa tare da halaka Hanifa kuma shari'ar ta tsaya saboda rashin lauyan wadanda ake zargin, Daily Trust ta ruwaito.
Bayan da alkali mai shari'a ya bayar da umarnin a samar musu da lauya, ya dage sauraron shari'ar zuwa ranar 14 ga watan Fabrairu mai zuwa.
Kisan Hanifa: An samu fusatattun matasan da suka bi dare, suka cinna wuta a makaranta
A wani labari na daban, rahotanni su na zuwa cewa wasu mutane sun banka wuta ga makarantar Noble Kids, wanda makashin Hanifa Abubakar ya mallaka.
Daily Nigerian ta bayyana cewa wasu mutane sun je wannan makaranta da ke kan titin Warshu Hospital a unguwar Kawaji, sun sa mata wuta.
Ana zargin dalilin yin hakan shi ne saboda mamallakin makarantar, Abdulmalik Tanko ya sace wata daliba mai shekara 5 a Duniya, ya kashe ta.
Asali: Legit.ng