Ke duniya: Ɗa ya doke mahaifinsa da taɓarya, ya aike shi barzahu a jihar Yobe
- Rundunar 'yan sandan jihar Yobe ta tabbatar da aukuwar mummunan al'amari a Masaba da ke karamar hukumar Bursari ta jihar
- Matashi mai suna Mai Goni dan shekaru ashirin a duniya ya halaka mahaifinsa mai suna Goni Kawu har lahira da tabarya
- Mugun dukan da Mai ya yi wa mahaifinsa a kai ne yasa ya samu miyagun raunika kuma aka garzaya da shi asibiti inda aka tabbatar da mutuwarsa
Bursari, Yobe - Rundunar 'yan sandan jihar Yobe a ranar Laraba ta ce wani matashi mai shekaru ashirin a duniya mai suna Mai Goni, ya halaka mahaifinsa mai suna Goni Kawu har lahira.
Mummunan al'amarin ya auku ne a garin Masaba da ke karamar hukumar Bursari ta jihar Yobe kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ASP Dungus Abdulkarim, ya sanar da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya cewa lamarin ya faru ne a ranar Talata wurin karfe bakwai da rabi na dare.
Daily Trust ta ruwaito cewa, ya ce Kawu mai shekaru sittin da biyar ya samu miyagun raunika a kansa sakamakon mugun dukan dan shi yayi masa da tabarya kuma an tabbatar da rasuwarsa a asibiti.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
ASP Abdulkarim ya ce wanda ake zargin ya tsere daga wurin da ya aikata barnar, inda ya tabbatar da cewa an tsananta bincike domin damko shi.
Matashi ya biya abokinsa N100,000 ya kashe mahaifinsa saboda ya gaji da jiran gado
A wani labari na daban, rundunar ‘yan sandan Najeriya na reshen jihar Neja sun kama wani matashi mai suna Abubakar Mohammed Buba da laifin kashe mahaifinsa.
Bayan shekaru 49, shahararren mai neman shugabancin kasa na PDP ya ziyarci garinsu da sunan zai tsaya takara
Jaridar Punch tace ‘yan sanda na zargin wannan matashi Abubakar Mohammed Buba mai shekara 25 da hannu wajen hallaka tsohon da ya haife shi.
Ana tuhumar Abubakar Mohammed Buba da biyan wani abokinsa kudi N110, 000 domin ya kashe mahaifinsa, wannan ya faru ne a Chachanga, a jihar Neja.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun yace Bida ya amsa laifinsa, yace ya yi haka ne saboda ya ci gadon dukiya.
A jawabin da DSP Wasiu Abiodun ya fitar a ranar Alhamis, ya bayyana yadda aka tsinci gawar marigayin da wanda aka biya kudi domin ya aika shi barzahu.
Asali: Legit.ng