Zulum ya gina gidaje 803 a Malari ya gwangwaje wadanda suka koma da N58.5m da kayan abinci
- Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya sake gina gidaje 803 a kauyen Malari inda mayakan ta'addancin Boko Haram suka fatattaki jama'a
- Kamar yadda gwamnan ya bayyana kowanne magidanci zai samu kyautar buhun shinkafa, masara, mangyada, katifa da kuma N200,000
- Hukumar Habaka yankin arewa maso gabas ta yi hobbasa inda ta gwangwaje jama'ar da tallafin kayan abinci da kudi
Konduga, Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum a ranar Laraba ya ziyarci kauyen Malari da ke karamar hukumar Konduga ta jihar Borno inda ya kaddamar da sake dawowar jama’ar yankin wadanda suka tafi gudun hijira kusan shekaru bakwai da suka gabata.
Komawarsu gidajensu ya biyo bayan sake gina musu gidaje dari takwas da uku da gwamnan ya yi bayan ‘yan ta’addan Boko Haram sun lalata su sakamakon miyagun farmakin da suka dinga kai musu.
Ma’aikatar gyara da mayar da ‘yan gudun hijiar gidajensu karkashin kwamishina Injiniya Mustafa Gubio ne suka jagoranci aikin sake gina gidajen.
Zulum wanda ya halarci bikin komawar jama’ar gidajnsu ya bayar da umarnin a baiwa magidanta dari biyar kudi har dubu dari. Wadannan ba su daga cikin wadanda suka koma gyararrun gidajen.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wadannene irin alkhairin da jama'ar suka samu?
Gwamnan ya kara da sanar da cewa za a bai wa wadanda suka koma gyararrun gidajen makuden kudi. Maza dari biyu da arba’in magidanta za su samu dubu dari biyu kowannensu yayin da mata 379 za su samu dubu goma da zani koda kuwa mazansu suna daga cikin wadanda suka samu kudin.
Zulum ya sanar da fara raba kayan abinci da kayayyakin bukata wanda ya ce Hukumar Habaka yankin Arewa maso Gabas ce ta dauka nauyi kuma ta bayar ne domin taimakawa wadanda suka dawo gidajensu.
Kowanne gida zai samu buhun masara, shinkafa, galan din mangyada, katifa da kuma karin zannuwa ga mata, kamar yadda Zulum ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Hotunan Zulum a sansanin 'yan gudun hijira na Bakassi, ya bai wa masu komawa gida N.5b
A wani labari na daban, Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya gwangwaje ‘yan gudun hijira fiye da mutane 5000 da rabin biliyan daya, Daily Trust ta ruwaito.
‘Yan gudun hijiran sun nuna bukatar komawa gidajensu ne don su cigaba da rayuwa. Gwamnan ya isa sansanin ‘yan gudun hijiran da misalin 5:45am inda aka fi sani da Bakassi a Maiduguri.
A takardar wacce hadimin gwamna Zulum ya saki, ya ce gwamnan ya yi sa’o’i 7 ya na jagorantar raba kudade da kayan abinci yayin da ya kai ziyarar ta ba-zata don tallafa wa mabukata da marasa gida saboda wasu mutanen su na zuwa sansanin ‘yan gudun hijiran tun safe sai dare su ke komawa gidajensu da sunan su ‘yan gudun hijira ne.
Asali: Legit.ng