Karar kwana: An shiga jimami yayin da matar tsohon mataimakin gwamna ta rasu
- Matar tsohon mataimakin gwamnan jihar Ondo ta riga mu gidan gaskiya bayan 'yar gajeruwar rashin lafiya
- Wannan na zuwa daga wata sanarwar da aka fitar, inda shugaban jam'iyyar APC a jihar ke bayyana ta'aziyyarsa
- Matar tsohon mataimakin gwamnan ta rasu ne tana da shekaru 77 a duniya, kamar yadda rahoto ya bayyana
Jihar Ondo - Alhaja Bejide, matar tsohon mataimakin gwamnan jihar Ondo, Alhaji Ali Olanusi, ta rasu.
Majiyoyin dangi sun ce ta rasu tana da shekaru 77 bayan ta yi 'yar jinya, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.
Majiyar ta ce mutuwar ta ta zo ne kwanaki kadan ga zagayowar ranar haihuwar mijinta.
Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Ondo ta bayyana rasuwar ta a matsayin babban rashi, abin mamaki da ban tausayi, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Shugaban jam'iyyar APC na jihar Ondo, Engr. Ade Adetimehin, a cikin wata sanarwa da ta fitar, ta ce marigayiya Bejide ta kasance ginshiki mai karfi da ke bayan nasarar da mijinta ya samu a siyasance.
Matar Shahararren Tsohon Gwamnan Najeriya Ta Rasu a Asibiti a Amurka
Njideka Ezeife, matar tsohon gwamnan jihar Anambra wanda kuma dattijo ne a kasa, Chief Chukwuemeka Ezeife ta riga mu gidan gaskiya.
Njieka ta rasu ne bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a wani asibiti da ke Amurka kamar yadda kungiyar dattawan Igbo ta sanar ta bakin sakatarenta Farfasa Charles Nwekeaku, The Sun ta ruwaito.
Nwekeaku ya ce ana sa ran tsohuwar matar gwamnan za ta dawo Najeriya ne a ranar Litinin, 13 ga watan Disamban 2021 amma kwatsam ta fara rashin lafiya.
A wani labarin daban, a ranar 6 ga watan Fabrairun bana ne Sarauniya Elizabeth II ta cika shekaru 70 a kan karagar mulkin Burtaniya.
Jaridar New York Times ta ba da rahoton cewa wannan ci gaba ya sanya sarauniyar cikin rukunin da ba a cika gani ba a tarihi, inda tarihi ya rubuta cewa, wasu sarakuna uku ne kawai aka san sun yi mulki sama da shekaru 70.
Kafar labarai ta CNN ta kara da cewa Elizabeth II, mai shekaru 95, ta zama sarauniyar Burtaniya ne bayan rasuwar mahaifinta King George VI a ranar 6 ga Fabrairu, 1952, yayin da take kasar Kenya a wani rangadi na kasa da kasa.
Asali: Legit.ng