Ortom ga Buhari: Ka dauki batun gwamnan Borno akan barnar ISWAP da gaske

Ortom ga Buhari: Ka dauki batun gwamnan Borno akan barnar ISWAP da gaske

  • Gwamna Samuwl Ortomb ya gargadi gwamnatin Muhammadu Buhari da ta dauki gargadin da Gwamna Babagana Zulum ya yi kan ISWAP da muhimmanci
  • Ortom ya ce ya kamata FG ta dauki matakan gaggawa don kora yan ta’addan daga Najeriya domin samun zaman lafiya
  • Tun farko dai gwamnan jihar Borno ya yi gargadin cewa kungiyar ISWAP na daukar karin mayaka

Benue - Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya shawarci gwamnatin tarayya da ta dauki gargadin da takwaransa na jihar Borno, Babagana Zulum, ya yi na cewa kungiyar ISWAP na daukar karin mayaka da muhimmanci, rahoton Daily Trust.

Ortom ya bayyana hakan ne yayin da yake tarban wata tawaga daga kungiyar agaji na VSF, a ranar Talata, 8 ga watan Fabrairu. Shugabar kungiyar, Misis Akerele Ogunsiji, ce ta jagoranci tawagar zuwa gidan gwamnati da ke Makurdi.

Kara karanta wannan

Kaduna: Jami'an tsaro sun ragargaji 'yan bindiga, sun kubutar da wadanda aka sace

Ortom ga Buhari: Ka dauki batun gwamnan Borno akan barnar ISWAP da gaske
Ortom ga Buhari: Ka dauki batun gwamnan Borno akan barnar ISWAP da gaske Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Gwamnan ya kuma yi kira ga gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu da su yi amfani da dabarun tsaro da zai tabbatar da komawar yan gudun hijira gidajensu ba tare da bata lokaci ba domin su ci gaba da harkokinsu yadda ya kamata.

Jaridar The Cable ta nakalto Ortom yana cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ina so na daga muryata a kan kokawar da takwarana na jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum ya yi game da ayyukan ISWAP a wannan yanki na kasar. Kada gwamnatin tarayya ta yiwa wannan lamari rikon sakainar kashi.
“A dauki matakan gaggawa don kora yan ta’addan daga Najeriya domin mu zauna lafiya. Ba za mu iya cigaba da zama a haka ba. Najeriya ta cancanci karin zaman lafiya fiye da wanda muke samu a yanzu."

Ya yi godiya ga VSF inda ya bayyana cewa:

Kara karanta wannan

Babu wani amfani: Masari ya nemi a bude iyakokin Katsina yadda aka bude na sauran Jihohi

“Tallafin da muke so a yanzu shine a bari mutanenmu da ke a sansanin yan gudun hijira su samu damar komawa mahaifarsu. Mutanenmu na son komawa garuruwansu don su koma rayuwa yadda ya kamata."

Tubabbun 'yan Boko Haram na taimakawa wurin yaki da ta'addanci, Zulum

A gefe guda, Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya ce kashi casa'in cikin dari na tubabbun yan Boko Haram da gaske sun ajiye makaman su sun bar ta'addanci.

Zulum ya bayyana hakan ne a wata tattauna wa da manema labaran gidan gwannati a ranar Laraba jim kadan bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da kwamitin dawo da 'yan gudun hijira gidajen su a arewa maso gabashiin Najeriya, a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Ra'ayin sa ya sha bambam da na takwaransa gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, wanda ya ce babu wani abu mai kama da tubabbun yan ta'adda, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gombe: Bayan kwanaki 30 a kasar waje, gwamna ya dawo tsaka da rikicin siyasa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng