Yanzu-Yanzu: Majalisa ta tabbatar da Farfesa Ayo Omotayo matsayin sabon shugaban NIPSS
- Majalisar dattawa ta tabbatar da nadin Farfesa Ayo O. Omotayo a matsayin darekta janar na cibiyar ilimin manufofi da dabaru na kasa, NIPSS da ke Karu cikin jos, Jihar Filato
- An samu wannan bayanin ne ta wata takarda wacce hadimin yada labarai na musamman ga shugaban majalisar dattawa, Ezrel Tabiowo ya saki ranar Talata
- Kamar yadda takardar ta nuna, an tabbatar da shi a mukamin ne bayan rahoton da kwamitin hadin-guiwa na harkokin ayyukan gwamnati da na kasa ta bayar akan nagartarsa
FCT, Abuja - Majalisar Dattawar Najeriya ta tabbatar da Farfesa Ayo. O. Omotayo a matsayin Direkta Janar ta Cibiyar Koyar da Manyan Ma'aikata, NIPSS da ke Kuru, Jihar Plateau.
An samu wannan bayanin ne ta wata takarda wacce hadimin watsa labarai na musamman ga shugaban majalisar tarayya, Ezrel Tabiowo, a ranar Talata ya saki.
A cewar sanarwar, an tabbatar da Omotayo ne bayan an yi nazari kan rahoton kwamitocin Ayyukan Gwamnati da Daidaito wurin nadin mukami da ayyukan gwamnati.
Kamar yadda takardar tazo, an tabbatar da nadin sa ne sakamakon rahoton da kwamitin hadin-gwiwa na harkokin ayyukan gwamnati da ta kasa ta bayar akan sa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
The Punch ta bayyana yadda mataimakin shugaban kwamitin, Sanata Danjuma La’ah yayin jawabi a maimakon shugaban kwamitin, Ibrahim Shekarau, ya kwatanta wanda aka zaba a matsayin jari wanda ya cika duk sharuddan da aka nema a sashi na 3 (2b) da 5 na cibiyar ilimin dabaru da manufofi na 2004.
Wanda aka nada bai taba samun matsala da jami’an tsaro ba
Ya ce wanda aka zaba ba ya da rahoto akan samun matsala da jami’an tsaro don haka aka amince aka nada shi a matsayin darekta janar na NIPSS.
A cewar La’ah:
“Daga DSS har ‘yan sanda sun gabatar wa da kwamiti rahotanni akan cewa bashi da wata matsala ta rashin gaskiya har yanzu da su.”
Daga bisani majalisar ta tabbatar da shi a mukamin.
Buhari: Na Ji Daɗin Yadda Masu Hannu Da Shuni Suka Gane Cewa Canja Najeriya Ba Aikin Mutum Ɗaya Bane
A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya yi farin cikin sanin cewa kusoshin Najeriya sun gane cewa canja kasar nan aikin kowa ne, The Cable ta ruwaito.
Kamar yadda kakakin shugaban kasa, Femi Adesina ya bayyana a wata takarda, Buhari ya yi wannan furucin ne a ranar Lahadi a wata liyafa ta girmama shugabannin kwamitin kasuwanci, siyasa, kafafen watsa labarai da sauran ma’aikata.
Dama a watan Janairun 2021 The Cable ta bayyana yadda Buhari ya zargi masu fada a jin kasar nan da kawo cikas ga gwamnatin sa.
Asali: Legit.ng