Kwamacala: Shugaban hukumar da aka tsige ya ki sauka daga kujera, ya bar wa Magajinsa
- Kwamacalar da ake fama da ita a hukumar nan ta PRODA ta ki ci, ta ki cinyewa har zuwa yanzu
- Tun 2020 aka sauke Fabian Okonkwo daga mukaminsa, amma har yanzu bai mika shugabanci ba
- An yi shugabanni barkatai bayan an kori Okonkwo; Agulana, Oriaku da wani Nathan Abia-Bassey
Enugu - A wani rahoto na musamman da jaridar Premium Times ta fitar, an ji cewa har yanzu an gaza shawo kan rikicin da ake fama da shi a hukumar PRODA.
Ofishin sakataren gwamnatin tarayya ya fitar da sakamakon binciken da ya yi a kan PRODA, an gano badakala, son-kai, satar kudi da laifuffuka iri-iri da aka yi.
Wanda ake zargi da duk wannan aika-aika shi ne tsohon shugaban hukumar ta PRODA, Charles Agulana wanda aka dakatar daga aiki a watan Nuwamban 2020.

Kara karanta wannan
Zargin matan asibiti da fasikanci: Budaddiyar wasika zuwa ga Dr. Abdallah Gadon-Kaya
An bukaci Charles Agulana ya sauka daga kujerarsa ya bar hukumar a hannun Fabian Okonkwo. Kwatsam sai aka ji an sauke Dr. Okonkwo daga rikon kwarya.
Bayan Minista ya nada Okonkwo a matsayin shugaban rikon kwarya, sai aka same shi da laifin korar ma’aikata, hakan ta sa aka maye gurbinsa da Arit Etukudo.
An yi waje da mutane biyu
Kafin a nada Dr. Fabian Okonkwo, jami’ai biyu sun yi kokarin rike shugabancin PRODA. Rahoton ya ce jami’an su ne Edwin Oriaku da kuma Nathan Abia-Bassey.

Source: UGC
Tun bayan wannan badakala aka nada Misis Etukudo a matsayin sabuwar shugabar hukumar tarayyar. Amma har yanzu Okonkwo bai mika mata ragamar aiki ba.
A wata takarda da aka aikawa Ministan kimiyya da fasaha na tarayya, an sanar da shi cewa Okonkwo ya tsere daga ofis bayan an bukaci Etukudo ta rike hukumar.
Martanin Dr. Fabian Okonkwo
Amma Okonkwo ya karyata zargin da aka jefe shi da shi a cikin wannan wasika mai lamba FMSTI/HM/2021/005/III, inda ya ce rashin lafiya yake damunsa.
Okonkwo ya kuma shaidawa manema labarai cewa an saba doka wajen sauke shi daga kujerarsa.
Hukumar BPP ta rubuta takarda ta na zargin Okonkwo da saba ka’idojin aiki a lokacin da yake ofis. Haka zalika EFCC ta na tuhumarsa da badakalar kwangiloli.
Zunuban Onu
Kwanaki an ji cewa an bankado irin badakalar da Dr. Ogbonnaya Onu yake tafkawa saboda damar da ya samu a gwamnatin. Ana zargin Ministan da sabawa dokar aiki.
Dr. Ogbonnaya Onu ya nada ‘yan majalisar da ke kula da hukumomi da duk cibiyoyin da ke karkashin ma’aikatarsa, har da wasu wadanda wa'adinsu bai kare ba.
Asali: Legit.ng
