Hana sa Hijabi a Kwara: Ba zamu lamunci wannan rainin hankalin ba: Kungiyar Musulmai
Kwara - Kungiyar Musulmai masu aikin jarida MMPN, reshen jihar Kwara, sun yi Alla-wadai da rikicin da ya biyo bayan hana dalibai mata sanya Hijabi a makarantar Oyun Baptist High School, Ijagbo.
Kungiyar tace kawo yanzu mutum guda ya mutu kuma da dama sun jikkata.
Shugaban kungiyar, Mallam AbdulRazaq Laaro, a jawabin da ya rattafa hannu, kungiyar ta bayyana cewa wannan abin takaici ne.
Cewar jawabin:
"Muna mamakin dalilin da zai sa mutum ko kungiya zasu gaza bin umurnin kotu da kundin tsarin mulkin Najeriya kan sanya Hijabi."
"Ta yaya sanya Hijabi zai shafi mutumin da ya zabi tafiya tsirara cikin makaranta ko waje."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
MMPN ta yi kira ga jami'an tsaro su zurfafa gudanar da bincike kan lamarin domin hukunta wadanda suka kaiwa Musulmai hari ranar zanga-zangar.
Hakazalika ta yi kira ga Gwamnatin jihar Kwara ta tashi tsaye ta dau mataki saboda kada rikici ya mamaye jihar.
Ba za mu bari ɗalibai mata su yi amfani da hijabi a makarantun mu ba, Kungiyar Kirista, CAN
Kungiyar kiristocin Najeriya, CAN reshen Jihar Kwara jiya ta jajirce akan cewa ba za ta taba barin amfani da hijabai a makarantun ta da ke jihar ba, The Nation ta ruwaito.
Ta nuna takaicin ta akan kungiyar wasu jiga-jigan musulmai a ranar Alhamis da ake zargin ta tayar da kura a makarantar Oyun Baptist.
Yayin tattaunawa da manema labarai a karamar hukumar Oyun, Rabaran Samuel Ajayi ya yi magana a maimakon kungiyar CAN inda yace ba za ta taba yarda daliban ta su dinga amfani da hijabi ba.
Mutum 1 ya mutu, da dama sun jikkata yayinda aka kaiwa Musulmai masu zanga-zanga kan hijabi hari
Mutum daya ya mutu, da dama sun jikkata yayinda aka farmaki iyaye masu zanga-zanga kan hana 'yayansu mata sanya Hijabi a makarantar Oyun Baptist High School, Ijagbo, karamar hukumar Oyun ta jihar Kwara.
Iyayen sun fito zanga-zanga ne saboda korar 'yayansu daga makarantar.
Wannan abu ya faru ranar Alhamis, 3 ga watan Febrairu, 2022, rahoton TheNation.
Zanga-zangar ta rikide ta koma rikici ne yayinda wasu da ake zargin Kiristoci ne suka fara jifan iyayen dake zanga-zanga a waje.
Hakazalika an sari daya daga cikin iyayen da adda.
Kakakin hukumar yan sandan jihar, Ajayi Okasanmi ya tabbatar da aukuwar rikicin.
Asali: Legit.ng