Ba mu bada sarauta haka kawai: Sarkin Daura yayinda yaiwa Amaechi 'Dan Amanar Daura'
1 - tsawon mintuna
- Kasar Daura ta cika ta banbatse ranar Asabar yayinda ake yiwa Ministan Sufuri nadin sarauta
- Amaechi ya bada gudunmuwa wajen ginin jami'ar Sufuri a Daura da layin dogon Katsina-Maradi dake gudana
- Shugaba buhari ya jinjinawa Rotimi Amaechi bisa wannan karramawa da masarautar Hausa tayi masa
Daura - An yiwa Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, nadin sarauta a matsayin Ɗan Amanar Daura a ranar Asabar, 5 ga watan Febrairu, 2022 a garin Daura, jihar Katsina.
Jiga-jigan siyasa, manyan jami'ar gwamnati, da wakilan Shugaba Muhammadu Buhari na halarci bikin nadin.
Amaechi da wani dan kasuwan Alhaji Nasiru Haladu Danu, ne Sarkin Daura, Dr Umar Farouk Umar, ya yiwa nadin.
Sarkin ya bayyana cewa an yi musu wannan sarauta ne bisa gudunmuwar da suka bada wajen cigaban kasa.
Yace:
"Masarautar ba ta bada sarauta haka kawai, sai mutanen da suka cancanta kwarai kamar wadannan mutanen biyu da muke baiwa yau."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Asali: Legit.ng