Kwara: Ba za mu bari ɗalibai mata su yi amfani da hijabi a makarantun mu ba, Kungiyar Kirista, CAN

Kwara: Ba za mu bari ɗalibai mata su yi amfani da hijabi a makarantun mu ba, Kungiyar Kirista, CAN

  • Jiya Kungiyar kiristocin Najeriya, CAN reshen Jihar Kwara ta nace akan ba za ta taba barin daliban ta su dinga amfani da hijabi a makarantun ta ba
  • Ta daura laifi akan wasu jiga-jigan musulmai akan rikicin da suka tayar a ranar Alhamis a makarantar Oyun Baptist da ke jihar
  • Yayin tattaunawa da manema labarai a karamar hukumar Oyun, Rabaran Samuel Ajayi ya yi magana a maimakon CAN inda yace sam ba za ta lamunci amfani da hijabi ba

Kwara - Kungiyar kiristocin Najeriya, CAN reshen Jihar Kwara jiya ta jajirce akan cewa ba za ta taba barin amfani da hijabai a makarantun ta da ke jihar ba, The Nation ta ruwaito.

Ta nuna takaicin ta akan kungiyar wasu jiga-jigan musulmai a ranar Alhamis da ake zargin ta tayar da kura a makarantar Oyun Baptist.

Kara karanta wannan

An kama wata mata a Kano tana yunƙurin sace yaro ɗan shekara 5 a hanyarsa ta zuwa makaranta

Kwara: Ba za mu bari ɗalibai mata su yi amfani da hijabi a makarantun mu ba, Kungiyar Kirista, CAN
Kwara: CAN ta ce ba za ta bari ɗalibai mata su yi amfani da hijabi a makarantun ta ba. Hoto: Kwara
Asali: Twitter

Yayin tattaunawa da manema labarai a karamar hukumar Oyun, Rabaran Samuel Ajayi ya yi magana a maimakon kungiyar CAN inda yace ba za ta taba yarda daliban ta su dinga amfani da hijabi ba.

Ajayi ya ce ba za su taba lamuntar amfani da hijabi ba a ko wacce makarantar su

A cewar Ajayi:

“Mun dade muna rokon gwamnati ta dawo mana da makarantun mu. Kuma muna so kowa ya san batun hijabin da muke tattaunawa akai, don haka ya kamata gwamnati ta tsahirta mana.
“Burin kallafa hijabi na makarantar Oyun Baptist ba zai taba cika ba don sun yi hakan ne saboda su tayar da kura. CAN din jihar zata ki amincewa don zamu yi yaki ko da da jinin mu ne.

Kara karanta wannan

An kashe ma'aikaciyar FIRS ranar da aka shirya bikin yi mata ƙarin girma a ofis a Legas

“Muna bukatar gwamnatin jihar ta dawo mana da makarantun mu cikin gaggawa. Kiristoci ma ‘yan asalin jihar ne don tamu ce gabadaya. Idan jihar ta ki amincewa zamu yi amfani da abinda kundin tsarin mulki ya tanadar don mu dawo da makarantun mu.”

Kungiyar musulman ta yaba da kokarin gwamnatin jihar

The Nation ta nuna yadda wata Kungiyar jiga-jigan Jihar Kwara ta musulmai ta bukaci gwamnatin ta shirya wata kwamiti wacce za ta binciko wadanda ke da alhakin halaka iyayen dalibai musulmai mata a Ijagbo yayin rikicin ranar Alhamis.

Kungiyar ta yaba da kokarin gwamnatin jihar akan jajircewa akan tilasta amfani da hijabi ga dalibai mata musulmai a duk wasu makarantu da gwamnatin jihar ta ke tallafa mawa.

Kungiyar ta tattauna da manema labarai a Ilorin akan batun tashin hankalin da ya auku ranar Alhamis a makarantar Oyun Baptist da ke Ijagbo a karamar hukumar Oyun cikin jihar.

Kara karanta wannan

Takara a 2023: Kungiyar CAN ta yi watsi da Yahaya Bello, ta yi karin bayani a kansa

Ana zargin tashin hankalin ya auku ne bayan hukumar makarantar ta hana dalibai mata musulmai amfani da hijabai a makarantar.

Ta bukaci a gano duk wadanda suke da alhakin kisan iyayen dalibai musulmai a Ijagbo

Ta yi kira akan yin gaggawar rufe makarantar sannan kuma a yi gaggawar mayar da daliban wasu makarantun har sai an shawo kan rikicin.

Shugaban kungiyar, Alhaji Isiaq Abdulkareem ya ce an halaka mahaifin daya daga cikin dalibai musulmai mata da ke makarantar, Habeeb Idris sannan kuma sauran iyayen dalibai 11 sun samu raunuka.

Kungiyar ta yi kira ga ‘yan sanda akan bincike don gano gaskiyar tarzomar kuma ayi gaggawar hukunta wadanda suka yi aika-aikar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164