Da dumi-dumi: Mayakan ISWAP 25 sun nitse a kogin Marte yayin da suke guje ma harin sojoji

Da dumi-dumi: Mayakan ISWAP 25 sun nitse a kogin Marte yayin da suke guje ma harin sojoji

  • Yan ta'addan ISWAP 25 sun nitse a wani kogi mai zurfi a yankin Marte da ke arewa maso gabas
  • Maharan sun hadu da ajalinsu ne yayin da suke tsere ma ruwan bama-bamai da rundunar sojin sama ke yi
  • Samamen sojin ya kuma dakile shirin kungiyar ta'addancin na kai manyan hare-hare kan sansanonin soji a yankin Arewa maso Gabas

Akalla mMayakan ISWAP 25 sun nitse a wani kogi mai zurfi a yankin Marte da ke tafkin Chadi a arewa maso gabas yayin da suke tserewa barin wuta da dakarun sojojin Najeriya ke yi ta sama.

Jiragen yakin sojojin, ciki harda Super Tucano na rundunar sojin sama, sun kai mamaya sansanin yan ta'addan a ranakun Laraba da Alhamis a hare-haren da ta shafe tsawon mako tana kaiwa.

Da dumi-dumi: Mayakan ISWAP 25 sun nitse a kogin Marte yayin da suke guje ma harin sojoji
Da dumi-dumi: Mayakan ISWAP 25 sun nitse a kogin Marte yayin da suke guje ma harin sojoji Hoto: Punch
Asali: UGC

Wani jami'in leken asiri da ke yankin ya sanar da PRNigeria cewa jiragen sun yi ta luguden bama-bamai ta sama a sansanoni da ma'ajiyar yan ta'addan na ISWAP.

Kara karanta wannan

Nasara: 'Yan sanda sun halaka 'yan ta'adda 23, sun yi ram da 'yan bindiga 37 a Sokoto

Ya ce:

“Jiragen yakin sojoji sun yi ruwan bama-bamai a Bukar Mairam da Jubularam, Abbaganaram da Chikul Gudu wanda ya yi sanadiyar tarwatsewar rumbunan ajiyar, inda yan ta’adda da dama suka mutu.
"Sai dai kuma, wadanda suka tsira a harin na Bukar Mairam da Jubularam, sun tsere sannan suka yi yunkurin tsallake wani kogi a tsakanin yankin tafkin chadi. A cikin haka ne kimanin su 25 suka nitse."

Ya ci gaba da bayyana cewa harin saman da sojoji suka kai a baya-bayan nan ya yi tasiri kan ISWAP, ya kuma dakile shirin kungiyar na kai wasu manyan hare-hare kan sansanonin soji a yankin Arewa maso Gabas, rahoton Daily Nigerian.

Innalillahi: 'Yan Boko Haram sun dasa bam a Borno, ya tashi da wani dan-sa-kai

Kara karanta wannan

NiMET: Akwai yuwuwar soke tashin jiragen sama masu zuwa Kano, Sokoto da Maiduguri

A wani labarin, wani jagoran kungiyar yan-sa-kai ya CJTF a jihar Borno ya rasa ransa sakamakon fashewar bam da ake zargin yan ta’addan Boko Haram da dasawa.

Wasu mutane biyar sun kuma jikkata a harin wanda ya afku a karamar hukumar Biu ta jihar Borno, Daily Trust ta rahoto.

Har zuwa mutuwarsa, marigayin, Ibrahim Maliya Saidu shine sakataren tsare-tsare na CJTF a Biu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng