Buhari ya ƙirƙiri sabuwar hukuma mai muhimmanci, ya naɗa shugabanta na farko
- Shugaba Muhammadu Buhari ya amince a kafa sabuwar Hukuma ta Kare Bayanai ta Kasa, NDPB
- Buhari ya ba da izinin ne bayan Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Isa Ali Pantami, ya mika masa bukatar yin hakan
- Har wa yau, Buhari ya amince da bukatar Farfesa Pantami ta nada Dr Vincent Olatunji daga Jihar Ekiti a matsayin Shugaban NDPB
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da kafa sabuwar hukumar gwamnati mai suna 'Nigeria Data Protection Bureau' (NDPB) mai kare bayanai da sirrin kasa a zamance.
Daily Trust ta rahoto cewa an kafa hukumar ne bayan Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Farfesa Isa Ali Pantami ya bukaci a kafa ta.
A cikin wata sanarwa da aka fitar a madadin Pantami, Uwa Suleiman, hadimansa bangaren watsa labarai ta ce an kafa NDPB ne bisa tsari mafi kyau kuma zai mayar da hankali ne don kare bayanai da sirrin kasa da wasu ayyukan.
Ya ce bayan samun nasarar aiwatar da tsarin zamantar da tattalin arzikin Najeriya na 'National Digital Economy Policy and Strategy' (NDEPS), hukumomi da dama sun zamantar da ayyukansu, rahoton Daily Trust.
"Hakan ya kara nuna muhimmancin samar da hukuma wacce za ta mayar da hankali kan kare bayanai da sirri," in ji shi.
NDPB za ta dora a kan nasarorin da aka samu a karkashin dokar tabbatar da kare bayanai ta kasa, sannan ta taimaka wajen samar da muhimman dokokin kare bayanai.
Buhari ya amince da Dr Vincent Olatunji a matsayin shugaban NDBP
Shugaba Buhari ya kuma amince da bukatar Pantami na nada Dr Vincent Olatunji a matsayin shugaban hukumar.
Dr Olatunji dan asalin Jihar Ekiti ne, kuma a lokacin da aka masa nadin, shi ne shugaban sashin eGovernment Development and Regulations Department a NITDA.
Nadinsa zai fara aiki nan take a cewar sanarwar.
Buhari: Na Ji Daɗin Yadda Masu Hannu Da Shuni Suka Gane Cewa Canja Najeriya Ba Aikin Mutum Ɗaya Bane
A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya yi farin cikin sanin cewa kusoshin Najeriya sun gane cewa canja kasar nan aikin kowa ne, The Cable ta ruwaito.
Kamar yadda kakakin shugaban kasa, Femi Adesina ya bayyana a wata takarda, Buhari ya yi wannan furucin ne a ranar Lahadi a wata liyafa ta girmama shugabannin kwamitin kasuwanci, siyasa, kafafen watsa labarai da sauran ma’aikata.
Dama a watan Janairun 2021 The Cable ta bayyana yadda Buhari ya zargi masu fada a jin kasar nan da kawo cikas ga gwamnatin sa.
Asali: Legit.ng