Gombe: Bayan kwanaki 30 a kasar waje, gwamna ya dawo tsaka da rikicin siyasa
- Bayan shafe kwanaki 30 a kasar waje, gwamna ya dawo, ya ga dandazon masoya, gwamnan jihar Gombe ya dawo domin cigaba da aikinsa a matsayin gwamna
- Gwamnan ya bar gari ne tun 3 ga watan Janairu, inda ya shafe kwanaki 30 yana hutu a waje, kuma ya dawo jiya
- Gwamnan ya samu tarbar masoya da magoya baya tun daga filin jirgin jihar har zuwa fadar gwamnatin jihar
Jihar Gombe - A ranar Alhamis ne Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Yahaya ya dawo jihar bayan shafe tsawon kwanaki 30 na hutu da ya yi.
Gwamnan ya bar jihar ne a ranar 3 ga Janairu, 2022, domin hutun aiki, ya kuma dawo ranar 3 ga watan Fabrairu a daidai lokacin da dimbin magoya bayansa suka yi dandazo a gidan gwamnati domin tarbarsa.
A cewarsa, wannan shi ne karo na farko tun da aka kafa gwamnatinsa da ya yi tafiya irin wannan, kamar yadda Punch ta rahoto.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yahaya ya kara da cewa:
"Mafi tsayin hutuna bai wuce tsawon makonni biyu ba."
Ya yabawa ‘yan jam’iyyar APC da jami’an gwamnati da matasa da mata da suka tarbe shi daga filin jirgin saman jihar zuwa gidan gwamnati, inda ya ce hakan na nuna hadin kan 'yan jihar.
Gwamnan ya kara da cewa matasa da mata sune kashin bayan tafiyarsa a siyasance inda ya yi alkawarin saka musu ta hanyar shayar dasu romon dimokuradiyya.
Gwamna ya tabbatar mana APC na nan daram a Gombe
Wakilin Legit.ng Hausa a jihar Gombe, ya tattauna da wani matashin jam'iyyar APC, Shamsudden Sani, inda ya bayyana irin jin dadi da kwarin gwiwarsa ga gwamnatin jihar.
Ya shaidawa wakilinmu cewa:
"Dawowar gwamna ya nuna har yanzu Gombe akwai APC, kuma kwalliya ta biya kudin sabulu.
"Gwamna ya ga dandazon masoya, tun daga filin jirgi har zuwa gidan gwamnati masoya ne da masu nuna goyon baya, wannan yake nuna 'yan Gombe suna tare da gwamna."
A wani labarin, rundunar ‘yan sandan jihar Gombe ta yi kakkausar gargadi ga jam’iyyun siyasa a jihar Gombe, inda ta bukace su da su daina duk wani nau’i na ayyukan da za su iya saba wa jadawalin yakin neman zabe.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ishola Babaita ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a jihar, Punch ta ruwaito.
Ya yi Allah-wadai da kone-konen rumfar APC da sakatariyar PDP da ofishin yakin neman zaben Atiku, da ke kan titin Gombe/Bauchi.
Asali: Legit.ng