Harin Boko Haram a Buratai: Shugaban Sojoji ya ziyarci Borno, ya tattauna da Sojoji

Harin Boko Haram a Buratai: Shugaban Sojoji ya ziyarci Borno, ya tattauna da Sojoji

  • Shugaban hafsun sojin Najeriya ya ziyarci jihar Borno domin ganawa da masu ruwa da tsaki a yankin kan yakar Boko Haram
  • Ya kai ziyarar ne bayan da 'yan ta'addan Boko Haram suka kai hari yankunan Biu da Burutai a cikin makon
  • Ya ziyarci masarautar gargajiya ta Biu, inda ya tattauna da sarkin na Biu kan lamurran da suka shafi tsaro

Jihar Borno - Babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Faruk Yahaya a ranar Alhamis ya fara ziyarar aiki a Arewa maso Gabas (NE), inda a halin yanzu sojoji ke jagorantar yaki da 'yan ta'addan Boko Haram da kuma ISWAP.

Wannan ziyarar aiki da kara kwarin gwiwa ga dakaru na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar Boko Haram/ISWAP ta kai hare-hare a garin Biu da kuma al'ummar Buratai inda jami'ar sojojin Najeriya ke da zama, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Zulum: Boko Haram za ta zama tamkar wasan yara idan aka bari ISWAP ta girma

Farukh Yahaya ya kai ziyara Borno
Harin Biu/Buratai: Shugaban Sojoji, Laftanar Janar Yahaya ya ziyarci jihar Borno | Hoto: thecable.ng
Asali: Facebook

Laftanar Janar Yahaya, ya bukaci dakarun da ke shiyyar Arewa maso Gabas (NE) da su kasance a ankare da kuma zama cikin shiri domin kawo karshen yakin da ake yi da masu tayar da kayar baya.

COAS, wanda ya isa hedikwatar rundunar sojin a Maiduguri, jihar Borno a ranar Laraba, 2 ga Fabrairu, 2022 tare da tawagarsa, daga bisani ya zarce zuwa garuruwan Biu da Buratai, inda ya tattauna da sojoji.

A wata sanarwa da daraktan hulda da jama’a na rundunar, Brig. Janar Onyema Nwachukwu, COAS ya yabawa sojojin bisa sadaukarwa da jajircewarsu wajen yaki da ta'addanci da tada kayar baya, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Ya kuma bukace su da su kara taka tsan-tsan tare da lura da nauyin da ya rataya a wuyansu, ya kara da cewa idan aka kara jajircewa za a kawo karshen yakin da ake yi a yankin Arewa maso Gabas.

Kara karanta wannan

ASUU ga FG: Ba za ku taba samun kwanciyar hankali ba, har sai mun sasanta

Ya kuma tabbatar wa da sojoji cewa za a ba su gudunmawar da suke ukata a kan kalubalen gudanarwa da aiki da ke fuskantar sassansu.

Ya ziyarci Sarkin Biu

A yayin ziyarar, ya kai ziyarar ban girma ga Mai Martaba Sarkin Biu, Alhaji Mai Mustapha Umar, a fadarsa, inda mai masaukin baki ya tabbatar wa COAS din goyon baya da hadin kai daga majalisarsa ta gargajiya da kuma al’ummar Biu.

Sarkin ya mika godiyar Masarautar ga COAS bisa sadaukarwa da jajircewar da sojoji suka yi wajen yakar ta'addanci a yankinsa.

Ya bukaci jami'an hukumar tsaron da su ci gaba da jajircewa wajen sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya dora musu.

Da yake jawabi a yayin ziyarar, COAS ya bayyana cewa, ya je fadar ne domin nuna girmamawa da kuma neman goyon bayan basaraken gargajiya da al’ummarsa kan ayyukan da ake yi na dakile ayyukan ta’addanci.

Ya kara da cewa hadin kai da fatan alheri na fadar da jama'ar kasa na da matukar muhimmanci a samun nasara mai ma'ana mai dorewa.

Kara karanta wannan

Kisan gilla: Bayan kisan Hanifa, wani Malami ya kashe Almajirinsa a jihar Kano

A wani labarin, Shugaba Muhammadu Buhari ya dira Maiduguri, babban birnin jihar Borno, domin ziyarar aiki ta kwana daya mintuna kadan bayan 'yan Boko Haram sun harba roka cikin filin jirgin sama na Maiduguri, Daily Trust ta ruwaito.

Manyan ma'aikatan gwamnati sun yi wa Buhari rakiya zuwa Borno, jirginsa ya dira a Maiduguri misalin karfe 11.45 na safiyar yau Alhamis.

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya na filin jirgin tare da dukkan shugabannin tsaro, da suka isa jihar domin tarbar Buhari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Tags: