Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun kai mummunan hari ofishin yakin neman zaɓen Ministan Buhari
- Mutane sun shiga tashin hankali a jihar Osun yayin da wasu yan ta'adda suka kai hari ofishin yaƙin neman zaɓen Rauf Aregbesola
- Wani shaidan gani da ido ya bayyana yadda maharan suka tada wuta ta hanyar buɗe wa wata Turansufoma wuta
- A cewarsa maharan su zo a motoci biyu bayan mambobin APC sun kammala taronsu na mako sun bar wurin
Ogun - Mutane sun shiga tashin hankali biyo bayan wani hari da yan bindiga suka kai ofishin da ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ke amfani da shi wajen yakin neman zaɓe.
Jaridar Punch ta rahoto cewa ministan na amfani da gidan Oranmiyan dake yankin Coca Cola, Osogbo jihar Osun, a matsayin ofishin yaƙin neman zaɓe.
Yan bindiga sun dira yankin da misalin ƙarfe 5:30 na yamma, kuma nan take suka buɗe wa ginin ofishin wuta.
Rahoton da muka samu ya nuna cewa maharan sun harbi wata Turansufoma dake bayan ofishin da kuma wata da aka kafa a gaban ofishin, wanda hakan ya tada wuta.
Jim kaɗan bayan kammala taron mako-mako da mambobin APC na tsagin Ministan ne aka tattaro cewa yan bindigan suka kai hari.
The Nation ta rahoto Wani shaidan gani da ido, Abosede Oluwaseun, yace:
"Jim kaɗan bayan taron yau, mutane sun bar wurin, yan bindigan suka zo a motoci biyu, Bas da kuma Sienna, suka aje su a ɗayan gefen."
"Na cikin motocin suka fito suka nufi ginin ofishin ɗauke da bindigu suka buɗe wauta. Ba zan iya ƙirga yawansu ba amma suna da yawa. Sun harbi Turansufoma dan kunna wuta cikin sa'a runfunan dake wurin suka kama da wuta."
"Mutanen da muka tara suka yi gaggawar kashe wutar bayan maharn sun tafi ta hanyar Gbogan/Osogbo."
A wani labarin na daban kuma Halin da ake ciki kan batun ɗan uwan Goodluck Jonathan da yan bindiga suka sace
A watan da ya gabata ne wasu miyagun yan bindiga suka yi garkuwa da ɗan uwan tsohon shugaban ƙasa, Jonathan a Bayelsa.
Sama da mako ɗaya da faruwar lamarin, wata majiya daga cikin iyalansa ta shaida cewa har yanzun maharan ba su tuntuɓe su ba.
Asali: Legit.ng