Ba na son cin haram, ana biya na kudin da ban yi aiki ba, Hadimin gwamna ya yi murabus
- Sale Ahmadu, hadimin gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku, ya yi murabus inda yace gwamnatin jihar ta rasa alkibla
- A cewar Ahmadu, shekaru 2 da yayi ya na aiki sun kasance mafi muni tare da barazana ga rayuwarsa da imaninsa
- Ya kara da cewa, ana ta biyansa kudi duk wata ba tare da wani aiki ba, hakan kuwa babbar barazana ce ga imaninsa
Taraba - Sale Ahmadu, mai bayar da shawara ta musamman ga Gwamna Darius Ishaku na jihar Taraba a ranar Alhamis, ya yi murabus inda ya ce gwamnatin jihar ta rasa alkibla.
Murabus din Ahmaadu ya zo ne kasa da wata daya bayan wani mataimaki na musamman ga gwamnana mai suna usman Sa'adu da wasu mutum biyu suka yi murabus, Punch ta ruwaito.
An aike wasikar murabus din ga gwamnan ta ofishin sakataren gwamnatin jihar, Anthony Jellason inda aka ce "shekaru biyu da suka gabata sun kasance masu matukar kalubale ga rayuwa ta da imani na.
"An biya ni albashi ba tare da wani aiki ba, wanda hakan ya ci karo da addini na ballantana a gwamnati da jam'iyyar da ta rasa alkibla.
“Mulkin jihar nan karkashin shugabancin Gwamna Ishaku tafe yake ba tare da wani cigaba ba.
“A don haka, ina so in shiga cikin wadanda suka saurari umarnin Ubangiji kuma suka cigaba da rayuwarsu."
A yayin martani ga murabus din, sakataren hulda da jama'a na Peoples Democratic Party (PDP), Honarabul Andeta'rang Irammae, ya musanta ikirarin cewa gwamnatin Ishaku ta rasa alkibla, Punch ta ruwaito.
Babbar Magana: Hadimin gwamnan Arewa da wasu jiga-jigan jam'iyyar APC sun yi murabus
A wani labari na daban, rikicin jam'iyyar APC reshen jihar Gombe ya ɗauki wani sabon salo ranar Laraba da daddare yayin da manyan jiga-jigan jam'iyya suka yi murabus.
The Nation ta rahoto cewa waɗan da suka yi murabus daga APC ɗin sun haɗa da, tsohon kwamishinan lafiya, Dakta Ahmed Gana, mai baiwa gwamna shawara, Dijjatu Bappa, da babban jigo Jamil Isyaka Gwamna.
Murabus da ficewa daga APC na Bappa da kuma Gwamna ya biyo bayan sauya shekar Dakta Ahmed Gana zuwa jam'iyyar PDP mai hamayya kwana biyu da suka shuɗe.
Asali: Legit.ng