Mutum 1 ya mutu, da dama sun jikkata yayinda aka kaiwa Musulmai masu zanga-zanga kan hijabi hari
- An kaiwa Iyaye Musulmai masu zanga-zanga hari a jihar Kwara, ana fargabar an yi rashin rai guda
- Iyaye sun fita zanga-zanga ne kan hana 'yayansu mata shiga makarantar Oyun Baptist kan Hijabi
- Gwamnatin jihar ta bada umurnin rufe makarantar zuwa lokacin da za'a kammala sulhu
Mutum daya ya mutu, da dama sun jikkata yayinda aka farmaki iyaye masu zanga-zanga kan hana 'yayansu mata sanya Hijabi a makarantar Oyun Baptist High School, Ijagbo, karamar hukumar Oyun ta jihar Kwara.
Iyayen sun fito zanga-zanga ne saboda korar 'yayansu daga makarantar.
Wannan abu ya faru ranar Alhamis, 3 ga watan Febrairu, 2022, rahoton TheNation.
Zanga-zangar ta rikide ta koma rikici ne yayinda wasu da ake zargin Kiristoci ne suka fara jifan iyayen dake zanga-zanga a waje.
Hakazalika an sari daya daga cikin iyayen da adda.
Kakakin hukumar yan sandan jihar, Ajayi Okasanmi ya tabbatar da aukuwar rikicin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya bayyana cewa yan sanda ba zasu bar wajen ba har sai sun tabbatar komai ya daidaita.
Me ya fito da iyaye zanga-zanga?
An tattaro cewa iyaye sun yi zanga-zanga ne sakamakon abinda shugabannin makarantar suka yanke cewa daga ranar 17 ga Junairu, za'a hana duk dalibar da ke sanye da hijabi shiga makarantar.
Kai tsaye gwamnatin jihar ta sanya baki inda ta umurci makarantar ta bar dalibai masu son sanya Hijabi su sa.
Matakin da gwamnatin jihar ta dauka
Gwamnatin jihar Kwara ta yi Allah-wadai da aukuwan wannan rikici.
Kwamishanar Ilimin jihar, Sa’adatu Modibbo Kawu tace gwamnatin jihar ta rufe makarantar gaba daya har ila masha Allahu.
Tace:
"Gwamnatin jihar ta yi Alla-wadai da rikicin da ya faru a makarantar gwamnatin Oyun Baptist dake Ijagbo, ranar Alhamis."
"Yayinda gwamnati da jami'an tsaro ke cigaba da kokari, an rufe makarantar har zuwa lokacin da aka kammala sulhu kan lamarin."
Asali: Legit.ng