'Yan Boko Haram sun kashe ɗalibai 167 da malaman makaranta 3 a Yobe, Gubana
- Gwamnatin Jihar Yobe ta ce mayakan kungiyar Boko Haram sun kashe dalibai 167 da malamai 3 a jihar
- Idi Barde Gubana, mataimakin gwamnan Yobe kuma shugaban kwamitin tattara kudade domin tallafawa ilimi ya sanar da hakan
- Gubana ya shaida wa manema labarai cewa gwamnatin na Yobe ta saka dokar ta baci a bangaren ilimi don farfado da ilimin
Jihar Yobe - Gwamnatin Jihar Yobe ta ce hare-haren yan ta'addar kungiyar Boko Haram ya yi sanadin mutuwar dalibai 167 da malamai uku a jihar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Wasu daliban 86 da malamai biyu sun samu munanan rauni sakamakon hare-haren da yan ta'addan suka kai musu a yunkurinsu na kawo karshen karatun boko a jihar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mataimakin gwamnan jihar kuma shugaban kwamitin tattara kudade domin tallafawa ilimi a jihar, Idi Barde Gubana, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin da ya ke yi wa manema labarai jawabi kan rahoton kwamitin.
An saka dokar ta baci a bangaren ilimi a Yobe
Rahoton Daily Trust ya bayyana cewa Gubana ya bayyana cewa kalubalen ne ya janyo gwamnatin jihar ta saka dokar ta baci a bangaren ilimi.
Ya ce an saka dokar ne bayan taro na ilimi da aka yi tare da kafa kwamitin kwararru domin farfado da ilimin firamare da sakandare a jihar.
Ya ce gwamnatin tana kokarin ganin ta inganta ilimi a jihar ta hanyar kara sabbin makaratun frimare da sakandare musamman domin yara mata da mutane masu bukata ta musamman.
A cewarsa, gwamnatin kuma tana da niyyar daukan sabbin malamai, bada horaswa da inganta walwala da jin dadin malamai a jihar.
'Yan bindiga sun sace mutane 29 a wani ƙauyen Katsina, 'Yan Sanda
Buhari ba zai iya tafiyar mota babu shiri ba, Fadar shugaban kasa ta yi wa PDP martani kan ziyarar Zamfara
A wani rahoton, kun ji cewa mutane 29 ne yan bindiga suka sace yayin harin da suka kai kauyen Godiya a cewar rundunar yan sandan Jihar Katsina.
Mai magana da yawun rundunar a jihar, Gambo Isah, ya tabbatar da adadin mutanen yayin zantawa da Channels Television a ranar Talata.
Wasu gungun yan bindiga ne suka kai hari a Ruwan-Godiya a daren ranar Lahadi a karamar hukumar Faskari.
Asali: Legit.ng