Sabon batu a shari'ar kisan Hanifa: An ce ba a je kotun da ya dace ba, an sauya kotu

Sabon batu a shari'ar kisan Hanifa: An ce ba a je kotun da ya dace ba, an sauya kotu

  • Yayin da ake jiran yanke wa makashin Hanifa Abubakar hukuncin da ya dace dashi a gaban kotu, wani batu ya sake fitowa
  • Masu shigar da kara sun nemi a kai karar gaban babban kotu don yin shari'ar da ta dace ba a kotun majistare ba
  • Wannan na zuwa ne a lokacin da ake zaman kotun a ranar Laraba a wata kotun majistare da ke jihar ta Kano

Jihar Kano - Barista Aisha Mahmoud, daraktar shigar da kara a jiya ta sanar da kotun majistare da ke tuhumar wasu mutane uku da suka kashe Hanifa Abubakar, cewa a dakatar da shari'ar bayan shigar da wata sabuwar kara a gaban wata babbar kotun Kano.

Jaridar This Day ta rahoto cewa, Aisha ta kara da cewa lauyan masu shigar da kara, ya shaida wa Alkalin kotun cewa:

Kara karanta wannan

Makashin Hanifa Abubakar: Kotu ta dage zaman hukunta AbdulMalik Tanko

“Mun shigar da karar ne, saboda laifin da ake zargin wadanda ake tuhumar sun aikata, wannan kotu ba ta da hurumin yin shari’ar."
Wadanda ake zargi da kisan Hanifa: Batu ya fara sauyawa a kotu
Sabon batu a shari'ar kisan Hanifa: An ce ba a je kotun da ya dace ba, an sauya kotu | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ta kuma yi bayanin cewa tuni Babban Alkalin Kano, ya mika karar zuwa babbar kotu mai lamba 5, kuma ana neman rushe karar farko da ke gaban kotun majistare.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bayan haka ne alkalin kotun ya dage zaman zuwa ranar 9 ga watan Fabrairun 2022, a shari’ar da ake yi wa Abdulmalik Tanko da wasu abokansa biyu bisa zargin kisan yarinyar mai shekaru biyar.

Daga nan ne babban alkalin kotun, Muhammad Jibril, ya bayar da umarnin a garkame wadanda ake kara a wani gidan gyaran hali.

Tanko tare da Hashimu Isyaku mai shekaru 37 da Fatima Musa mai shekaru 26, an gurfanar da su a gaban kotu bisa tuhume-tuhume hudu da suka hada da kisan kai, hada baki, garkuwa da mutane da boye yarinya.

Kara karanta wannan

Maganar kashe Hanifa ta shiga majalisar wakilai, an caccaka tsinke kan nema mata adalci

Wani Malami ya azabtar da dalibinsa har ta kai ga ya mutu

Yayin da ake ci gaba da jimamin kisan Hanifa, Daily Trust ta rahoto cewa, gwamnatin jihar Kano ta bukaci a tono gawar wani yaro Almajiri da aka ce malaminsa ya azabtar da shi har ya mutu.

Dakta Muhammad Tahar Adamu, kwamishinan harkokin addini ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ziyarci makarantar da ke unguwar Wailari a jihar Kano, ranar Talata.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an kama wasu da ake zargi da hannu a lamarin.

Ya kara da cewa ‘yan sandan sun kai samame ne a wata haramtacciyar cibiyar gyaran hali a unguwar Naibawa ‘Yan Lemo da ke karamar hukumar Kumbotso.

A wani labarin, wata jami'a a jamhuriyar Nijar, Maryam Abacha American University ta sanyawa wani titi sunan Hanifa Abubakar Abdulsalam.

Kara karanta wannan

Rudani: Matar Atiku ta koka kan yadda yaransa ke barazanar kasheta don ta nemi saki

Hanifa Abubakar, wata yarinya mai shekaru 5, an yi mata kisan gilla a jihar Kano, bayan da wani malami kuma shugaban makaranta ya sace ta.

Bayan kisan Hanifa, jama'a da dama sun damu matuka kan labarin, lamarin da ya kai ga tsoma baki daga gwamnatin Kano da ma na Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.