Ba shugaba da mataimaki a kasa: Buhari zai shilla Habasha, Osinbajo kuma Ghana
- Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo zai shillah kasar Ghana domin halartar wani taron kasashen Afrika
- Wannan na zuwa ne daidai lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tafi kasar Habasha halartar taro makamancin wannan
- Ana sa ran mataimakin shugaban kasar zai dawo yau bayan kammala caccaka tsinke a taron da Buhari ya tura shi
Abuja - Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo zai halarci wani babban taro na musamman na kungiyar ECOWAS a birnin Accra na kasar Ghana a yau Alhamis, The Nation ta ruwaito.
Labarin tafiyarsa ta fito ne a cikin wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai na ofishin mataimakin shugaban kasa, Laolu Akande ya fitar.
Sanawar ta ce Osinbajo ne zai wakilci Najeriya yayin da kungiyar ta kasashen yammacin Afirka za ta tattauna kan harkokin siyasa a Burkina Faso, Mali da Guinea.
A cewar rahoto, taron zai yi nazari kan rahoton tawagar ECOWAS da ta aike zuwa Quagadougou domin ganawa da gwamnatin mulkin soja da ta kwace mulki a Burkina Faso kwanan nan. .
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Taron dai zai samu halartar shugabannin kasashen yankin da za su duba yiwuwar kakabawa kasar karin takunkumi bayan dakatar da ita daga kungiyar a makon jiya.
Aukuwar juyin mulki a Nahjiyar Afrika
A ranar Litinin din da ta gabata ne sojoji suka tilasta wa zababben shugaban kasar Burkina Faso Roch March Kabore barin mukaminsa a wani juyin mulki da suka yi, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
Kwace mulkin da sojoji suka yi a Burkina Faso ya biyo bayan irin abin da ya faru a Mali da Guinea kwanan nan.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika wa mataimakin shugaban kasar wakilcin Najeriya a taron shugabannin kungiyar ECOWAS kan batutuwan da suka shafi rugujewar demokradiyya da dawowar mulkin soja a yankin.
Mataimakin shugaban kasar zai samu rakiyar karamin ministan harkokin waje, Ambasada Zubairu Dada; Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin tattalin arziki, Dr. Adeyemi Dipeolu da sauran manyan jami'an diflomasiyyar Najeriya.
Ana sa ran mataimakin shugaban zai dawo Abuja a yau.
A rahoton Legit.ng Hausa na baya, kunji cewa, shugaba Muhammadu Buhari a ranar Alhamis zai shilla Addis Ababa, babbar birnin kasar Habasha domin halartan taron gangamin gamayyar kasashen Afrika na 35.
Wannan na kunshe cikin jawabin da mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya saki da yammacin Laraba.
Bayan taron, shugaba Buhari zai zauna da wasu shugabannin kasashe kan ganin yadda za'a bunkasa huldar kasuwanci, karfafa tsaro, dss.
Asali: Legit.ng