Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari zai tafi Habasha halartan taron gamayyar kasashen Afrika
- Shugaba Buhari zai halarci taron gangamin shugabannin kasashen nahiyar Afrika AU
- Shugaban kasa zai samu rakiyar Ministoci hudu, manyan jami'ai biyu da kuma sauran hadimai
- Yan Najeriya sun yiwa shugaban kasan fatan Allah ya kiyaye hanya
Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Alhamis zai shilla Addis Ababa, babbar birnin kasar Ethiopia domin halartan taron gangamin gamayyar kasashen Afrika na 35.
Wannan na kunshe cikin jawabin da mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya saki da yammacin Laraba.
Bayan taron, shugaba Buhari zai zauna da wasu shugabannin kasashe kan ganin yadda za'a bunkasa huldar kasuwanci, karfafa tsaro, dss.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Adesina yace Buhari zai samu rakiyar Ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama; Ministan Lafiya, Osagie Ehanire; Ministan Noma, Mohammed Abubakar; da Ministar tallafi da jin kai, Sadiya Farouq.
Sauran sun hada da NSA Maj. Gen. Babagana Monguno da Shugaban hukumar NIA, Amb. Ahmed Rufai Abubakar.
Arewa zata ga canji cikin yan watanni masu zuwa, Shugaba Buhari
A wani labarin kuwa, Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya tabbatarwa yan Najeriya cewa zasu ga canji a watanni kaɗan masu zuwa musamman a arewa maso gabas.
Buhari ya tabbatar da cewa mutane zasu ga canji daga matsalar ayyukan ta'addanci zuwa zaman lafiya da samun cigaba a yankunan da suke rayuwa.
Shugaban Buhari ya yi wannan furucin ne bisa alƙawarin da ya yi a 2015, na dawo da zaman lafiya a Arewa ta gabas da kuma ɗora yankin kan hanyar cigaba da bunƙasa.
Asali: Legit.ng