Tsohon shugaban hukumar yakin rashawa a Kano, Muhuyi Rimin Gado ya shigar da Ganduje Kotu
- Kwanaki Bayan komawa PDP, Muhuyi Rimin Gado ya shiga kotu don kwato hakkinsa daga wajen gwamnatin Kano, a cewarsa
- Tsohon mayakin rashawan ya bayyanawa kotu cewa ana masa bita da kulli da barazana
- Gwamna Abdullahi Ganduje ya dakatad da Muhuyi Rimin Gado daga kujerarsa a tsakiyar 2021
Abuja - Dakataccen shugaban hukumar amsa korafi da yaki da rashawa na jihar Kano, Muhuyi Rimin-Gado, ranar Laraba ya shigar da Ganduje kotun ma'aikata kan korarsa da akayi daga bakin aiki.
Daga cikin wadanda ya shigar karar akwai Antoni Janar na jihar Kano, majalisar dokokin jihar Kano, Akawunta janar na jihar Kano, shugaban hukumar, Mahmud Balarabe, da kwamishanan yan sandan jihar.
Kamfanin dillancin labarai NAN ya ruwaito cewa Alkali mai shari'a Oyejoju Oyewumi ya saurari kara.
Lauyan Rimin-Gado, Muhammad Tola, ya bayyanawa kotu cewa an sanar da dukkan wadanda aka shigar kotu amma basu amsa ba.
Amma lauyan Gwamna Ganduje, Abdulsalam Saleh, ya sanarwa kotu cewa tuni sun nemi uzuri kan hakan.
Ya kara da cewa sun nemi izinin a dawo da zaman jihar Kano tunda duka wadanda aka shigar kara na Kano.
Alkalin ya dage zaman zuwa ranar 7 ga Maris don tabbatar da an sanar da kowa.
Rimin-Gado ya koma PDP
Muhyi Rimin-Gado, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar People Democratic Party (PDP) gabannin zaben 2023.
Rimin-Gado ya bayyana cewa ya mika takardar neman shiga PDP ta yanar gizo yayin da yake sa ran yin rijista a unguwarsa ta karamar hukumar Rimingado a watan Fabrairu, jaridar Punch ta rahoto.
Tun bayan dakatar da shi da gwamnatin jihar Kano ta yi a ranar 5 ga watan Yulin 2021, fastocin tsohon shugaban na hukumar yaki da cin hanci sun karade unguwanni a Kano inda suke ayyana aniyarsa na takarar gwamna a zabe mai zuwa.
Yayin da wasu daga cikin fastocin suka bayyana babu tambarin kowace jam'iyya, sauran na dauke da tambarin APC.
Asali: Legit.ng