Matasa sun bayyana sunan gwamnan da suke zargi da hannu a harin yan bindiga

Matasa sun bayyana sunan gwamnan da suke zargi da hannu a harin yan bindiga

  • Matasan yankin karamar hukumar Shiroro sun zargi gwamnatin jihar Neja da laifi kan harin da yan bindiga suka kai yankin su
  • A martanin da kungiyar matasa ta yi wa gwamnan jihar, matasan sun ce gwamnati na zargin mutane ne saboda kokarin boye gazawarta
  • A harin dai yan bindiga sun kashe aƙalla mutum 20 da kuma jami'an tsaro 11 a ƙauyen Galadima Kogo

Niger - Matasan ƙaramar hukumar Shiroro a jihar Neja sun zargi gwamnatin jihar su da laifi kan harin da yan ta'adda suka kai yankin su ranar Asabar da ta gabata.

Daily Trust ta tattaro cewa yayin harin yan ta'addan sun kashe akalla mutum 20 tare da jami'an tsaro 11 a ƙauyen Galadima-Kogo.

Matasan sun yi wannan zargin ne yayin martani ga jawabin gwamna Abubakar Sani Bello, ta hannun sakataren watsa labaransa Mary Noel-Berje.

Kara karanta wannan

Nasara: 'Yan sanda sun halaka 'yan ta'adda 23, sun yi ram da 'yan bindiga 37 a Sokoto

Gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello
Matasa sun bayyana sunan gwamnan da suke zargi da hannu a harin yan bindiga Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Yayin da yake tsokaci kan harin, Gwamna Bello ya zargi mutanen dake zaune a ƙauyukan Galape da Kudodo da laifin ƙin sanar da jami'an tsaro yayin da suka gano yan ta'addan na kan hanyar zuwa garin.

Amma kungiyar matasan Shiroro, a wata sanarwa da suka fitar ranar Talata, ɗauke da sa hannun Abubakar Yusuf Kokki da Bello Ibrahim, sun musanta zargin gwamnan.

Martanin matasan ga kalaman gwamnati

Hakanan sun kuma zargi gwamnan da gwamnatinsa tare ɗa jami'an tsaro da rashin sanin makamar aiki.

A sanarwan, matasan suka ce:

"A matsayin waɗan da wannan mummuna lamarin na rashin imani ya faru da mu, kalaman gwamnati cin mutunci ne a hankalce."
"Hannun riga da ikirarin gwamnati, mutane sun sanar da hukumomi damuwarsu kan yuwuwar kawo hari saboda yan ta'adda na shawagi zuwa yankin Galadima Kogo."

Kara karanta wannan

An gano gawarwakin mutane 30 da suka fara ruɓe wa a wani asibiti a Rivers

"Amma maimakon gwamnati ta ƙara tsaurara tsaro, sai ta kwashe jami'an tsaron dake yankin da kai su wani wuri daban. Muna da yaƙinin hakan ba zai rasa nasaba da wata manufa ba ta daban."

Ƙungiyar matasan ta ƙara da cewa zargin mutanen ƙauye da gwamnatin jiha ta yi, wani kokari ne na ɓoye gazawarta wajen kare rayukan al'umma.

Ɗaruruwan mutanen ƙauye sun bar mahallinsu a karamar hukumar Shiroro saboda taɓarɓarewa tsaro.

A wani labarin kuma Pantami ya faɗi babban abinda yan bindiga ke amfani da shi wajen ayyukan ta'addanci a Arewa

Minsitan sadarwa a Najeriya, Farfesa Isa Ali Pantami, yace yan bindiga na ribatar yawan faɗin kasa a jihohin arewa maso gabas wajen aikata ta'addanci.

Pantami yace hudu daga cikin jihohin Najeriya shida da suka fi faɗi duk suna yankin arewa maso gabas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262