ASUU ga FG: Ba za ku taba samun kwanciyar hankali ba, har sai mun sasanta

ASUU ga FG: Ba za ku taba samun kwanciyar hankali ba, har sai mun sasanta

  • Kungiyar malamai masu koyarwa na jami'o'i, ASUU ta sanar da gwamnatin tarayya cewa ba za ta samu kwanciyar hankali ba sai ta sasanta da su
  • ASUU ta zargi gwamnatin tarayya da alkawarin da ba ta cikawa tare da kwarewa wurin shirya karairayi domin kare kansu
  • Kungiyar ta ce ta dade ta na alkawari da sa hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da gwamnatin tarayya amma ba a cika wa

Kungiyar malamai masu koyarwa na jami'o'i, ASUU, a jiya ta sanar da gwamnatin tarayya cewa ba za ta samu kwanciyar hankali ba har sai ta sasanta da su kan halin da ilimin jami'o'i ke ciki.

A wata zantawa da manema labarai a Awka, shugaban ASUU na jami'ar Nnamdi Azikiwe, Comrade Stephen Ofoaror ya ce ya gane yadda ake neman barazana ga zaman lafiyan kasar.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: ASUU ta ce ba karatu ranar Litinin a BUK, za a tara dalilai da iyaye a yi musu bayani

Vanguard ta ruwaito cewa, inda ya ja kunne a kan bakar guguwar da ta taso sanadiyyar gazawa wurin cika alkawarin da gwamnatin tarayya ta dauka na girmama yarjejeniyar da ta yi da ASUU a ranar 23 ga watan Disamba, 2020.

ASUU ga FG: Ba za ku taba samun kwanciyar hankali ba, har sai mun sasanta
ASUU ga FG: Ba za ku taba samun kwanciyar hankali ba, har sai mun sasanta. Hoto daga vanguardngr.com
Asali: UGC
Ya ce: "Idan za a tuna lokacin da aka yi kokarin sa ASUU ta janye yajin aikin da ya dauki tsawon watanni tara (tun daga watan maris na 2020 zuwa watan Disamba 2020), shigar da yarjejeniyar fahimta (MOU) tsakanin wadanda suka wakilci gwamnatin tarayyar Najeriya da shugabannin ASUU a ranar 22 ga watan Disamba, 2020.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Mun tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ta dauka sama da shekara daya ta na karya duk alkawuran da ta dauka a takardar yarjejeniyar.
"Kamar yadda halinsu ya fito fili, gwamnatin tarayyar Najeriya ta karya alkawarin da ta dauka bayan ta sa hannu a kan canza yarjejeniyar da ke tsakanin ta da ASUU a shekarar 2009. Hakuri da kau da kan da ASUU ta ke da shi ne yasa suka kafa yarjejeniyar fahimta daban-daban, amma duk da haka gwamnatin tarayyar ba ta yi kasa a guiwa wurin ganin ta karya alkawuran ba.

Kara karanta wannan

Ba na son cin haram, ana biya na kudin da ban yi aiki ba, Hadimin gwamna ya yi murabus

"A yanzu da muke magana, gwamnatin tarayyar ta gaza cika muhimman alkawuran da ta dauka bayan yarjejeniyar fahimta na shekarar 2009 da ke tsakanin ta da ASUU, wanda ya hada da: samar da kudade domin farfado da jami'o'in gwamnati, biyan alawus da zai taimaka wa ilimin boko, da kuma sa hannu a kan sulhu game da yarjejeniyar da suka yi ta shekarar 2009."
"Al'amarin ya yi kamari ne lokacin da aka gabatar da tsarin IPPIS inda hakan ya tarwatsa gami da lalata albashi, rashin biyan hakkin malamai na tsawon lokaci da rashin amsar mafitar da UTAS ta kawo domin biyan hakkin ma'aikata a jami'oi".

Ya ce a 1 ga watan Fabrairu, 2022 mambobin ASUU suna bin bashin tsakanin albashin wata 1 zuwa shekaru 2, inda ya kara da cewa, al'amarin ya fi kamari a wasu jami'oin jiha, musamman kudu maso gabas wanda ya hada da; jami'ar Odumegwu Ojukwu ta jihar Anambra inda babu tsarin biyan fansho, kuma ba a bada alawus don karfafawa ilimi da dai sauran su.

Kara karanta wannan

Ohworode na masarautar Olomu: Muhimman abubuwa 5 game da basarake mai shekara 105

Ofoaror ya bayyana tsananin rashin jin dadinsa a kan duk iya kokarin da sukayi na ganin gwamnati ta saurare su don shawo kan matsalolin, amma sai dai hakan bai yuwu ba, inda ya kara da, "Sai dai wakilan gwamnatin tarayyar Najeriya da suke ta barazana ga yarjejeniyar alkawarin da kuma yarjejeniyar fahimta."

"Muna amfani da wannan damar domin kira ga duk wanda ya amsa sunan sa dan Najeriya, wadanda suka hada da shuwagabannin addini, sarakunan gargajiya, iyaye, dalibai, kungiyoyin ma'aikatan gwamnati(CSO) da duk wani mai mukami da su fadawa gwamnatin tarayya ta cika alkawarin yarjejeniyar da ta yi da ASUU don tseratar da makarantun gwamnati daga yajin aiki.
"Muna rokon kungiyoyin dalibai, iyaye da sauran mutane da su taya ASUU a wannan fadi tashin domin ceto makarantun mu na gwamnati kafin a zo kan makarantun sakandare da firamaren gwamnatin Najeriya.
"Muna sane da yadda fiye da kashi 95% na ma'aikatan gwamnati suke tura yaran su jami'oin kasar waje da kudin harajin da aka biya, amma sun ki zuba kudi a jami'oin gwamnatin. Ba za mu bar haka ya cigaba ba.

Kara karanta wannan

Tafiya a mota: Gwamna ya makale a hanyar Kaduna, jirgi ya dauke shi cikin gaggawa

"Mun kara sanar da y'an Najeriya, idan ba gwamnatin tarayya ta shawo kan matsalolin ba, hankulan mu baza su taba kwanciya ba.
"Ba za mu kara yarjejeniyar fahimta da yarjejeniyar alkawari ba. Idan aka fara yakin, ba za a dakata ba har sai an biya mana dukkanin bukatunmu.
"Rashin gaskiyar gwamnatin tarayyar ba abu bane da wanda aka kasa ganewa, ya wuce wanda za a iya jurewa" a cewarsa

Zuƙi ta malle: ASUU ta magantu kan ikirarin FG na bata N52.12bn

A wani labari na daban, kungiyar malamai masu koyarwa na jami’o’i na kasa, ASUU ta musanta maganar ministan kwadago da ayyuka, Chris Ngige, wanda ya ce N52.12b suka sakar wa kungiyar.

Daily Trust ta ruwaito cewa, kungiyar ta kwatanta maganarsa a matsayin kalaman yaudara da ha’inci wadanda ya furta musamman don bata kungiyar a idon jama’a.

Yayin hira da manema labarai a ranar Laraba, mai gudunarwar kungiyar na shiyyar Kano, Kwamaret Abdulkadir Muhammad, ya ce N22.17b kadai gwamnati ta sakar wa kungiyar na alawus din ma’aikatan wanda a ciki 75% (N16.6bn) ne kadai na ‘yan kungiyar, yayin da sauran 25% din na sauran kungiyoyi ne.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Likitocin Najeriya sun sake bijiro da bukata, sun gargadi gwamnati

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng